Ka zo mu baka nasara a zaben 2019 - Guru Maharaji ya fadawab Buhari

Ka zo mu baka nasara a zaben 2019 - Guru Maharaji ya fadawab Buhari

- Shugaba kuma mutumin da ya kafa wani addini mai taken 'soyayya ga iyali', Satguru Maharaji Ji, ya bayyana goyon bayansa ga kudirin shugaba Buhari na neman tazarce a zaben 2019

- Sai dai ya bayyana cewae dole jam'iyyar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari su je gare shi domin neman tubaraki da sa'a

- A cewar Mahaji Ji, "Zan zabi jam'iyyar APC da shugaba Buhari saboda yakinsa da ya ke yi da cin hanci da kuma gaskiyar da ya ke nunawa a kokarinsa na ciyar Najeriya gaba

Shugaba kuma mutumin da ya kafa wani addini mai taken 'soyayya ga iyali', Satguru Maharaji Ji, ya bayyana goyon bayansa ga kudirin shugaba Buhari na neman tazarce a zaben 2019.

Sai dai ya bayyana cewae dole jam'iyyar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari su je gare shi domin neman tubaraki da sa'a matukar suna son yin nasara a zaben shekarar 2019.

Maharaji Ji na wadannan kalamai ne yayin da Mahraji Ji da tawagar jama'ar sa su ka kai ziyara ofishin jaridar The Nation jiya, a jihar Legas, a ciga da shirye-shiryen wani babban gangamin da mabiya addininsu ke yi a wannan watan.

Ka zo mu baka nasara a zaben 2019 - Guru Maharaji ya fadawab Buhari
Satguru Maharaji
Asali: Twitter

A cewar Mahaji Ji, "Zan zabi jam'iyyar APC da shugaba Buhari saboda yakinsa da ya ke yi da cin hanci da kuma gaskiyar da ya ke nunawa a kokarinsa na ciyar Najeriya gaba.

"Yana bukatar goyon baya da taimakon mu. Shine shugaban kasa na farko a tarihin nahiyar Afrika da ya yi bajintar da babu wanda ya taba irinta."

DUBA WANNAN: Sojoji sun gano wani haramtaccen sansanin bayar da horon soji a arewa

Ya kara da cewar barin Buhari ya maimaita mulki zai bawa mutanen arewa kwanciyar hankali ta fuskar samun adadin shekarun da kudu ta yi na mulkin Najeriya tun bayan dawowar dimokradiyya.

Sai dai Maharaji Ji ya sanar da APC dashugaba Buhari cewar mtukar suna bukatar nasara a zaben 2019, dole su je gare shi domin neman sa'a.

Kazalika ya gargadi 'yan da su kula sosai wajen zaben shugabanni a zaben 2019, yana mai bayyana cewar wasu na son dawowa gwamnati ne domin kawai su cigaba da cin hanci da rashawa kamar yadda su ka yi a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel