G100: Atiku, Peter Obi Suna daf da Tsaida ‘Dan Takara 1 da Zai Tunkari Tinubu
- Gamayyar G100 mai kokarin hada kan adawa ta yi nisa wajen tsaida ‘dan takara guda a 2027
- Shugaban jam’iyyar SDP na kasa ya ce magana ta yi nisa tsakanin wasu jam’iyyun hamayya a kasar
- Jam’iyyun adawan da ake tattaunawa da su sun kunshi ADC, NDC sai kuma PDP, SDP da NRC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jagororin adawa suna tattaunawa domin ganin sun fito kansu a hade a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wasu daga cikin ‘yan hamayya suna so jam’iyyun adawa su fito da ‘dan takara guda da zai kara da Bola Ahmed Tinubu.

Source: Getty Images
G100 tana hada kan masu neman shugaban kasa
Labarin da muka samu a jaridar Daily Trust ya ce kungiyar G100 ta yi ikirarin cewa ta kusa cin ma wannan nufi.
Gamayyar G100 ta ‘yan adawa ta ce an samu cigaba sosai a kokarin da ake yi na hada kan ‘yan takaran 2027.
Atiku Abubakar, Peter Obi, da Donald Duke suna cikin ‘yan takaran da a tsakaninsu G100 za ta tsaida daya.
'Yan adawa sun yi zama a inuwar G100
A ranar Larabar nan, Shugaban jam’iyyar SDP, Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe ya fadi cigaban da ake samu.
Farfesa Sadiq Abubakar Gombe ya yi bayani wajen kaddamar da kwamitocin yada labarai da na shari’a na gamayyar.
Ya ce G100 ta tattauna da jagororin jam’iyyu da masu neman takarar shugaban kasa da nufin a samu hadin-kai.
Abin da 'yan adawa suke shirin yi
Makasudin shi ne a fito da ‘dan takaran da ake ganin zai iya doke APC a takarar shekarar 2027.
“Burinmu shi ne gabatar da ‘dan takaran da zai iya doke APC a kafa gwamnati mai zuwa. Kuma mun yi nisa sosai a kan wannan.”
- Farfesa Sadiq Abubakar Gombe
Farfesan ya ce suna fatan cewa kafin zaben 2027 za su cin ma matsaya a kan abubuwan da yanzu aka kakare a kansu.
A cewarsa, rantsar da kwamitocin ya nuna tafiya ta yi nisa wajen ganin kan ‘yan adawa ya hadu, sun fito da mutum guda.
Su wane ne jam'iyyun da ake tattaunawa da su?
Vanguard ta ce G100 ta kunshi jam’iyyun ADC, NDC, PRP, SDP, PDP da APM wadanda duk suna takarar shugaban kasa.
Wasu cikin shugabannin jam’iyyun nan sun halarci zaman da aka yi na kaddamar da kwamitocin gamayyar adawar.
Abubuwan da 'yan adawan za su duba
Rahoton ya ce gamayyar ta G100 ba ta fadi yadda za ta bi wajen fito da ‘dan takaran da zai gwabza da Bola Tinubu ba.
Ana dai sa ran cewa da tattaunawan da ake yi, ‘yan takaran za su hakura su gabatar da mutum daya ya shiga gaba a 2027.
‘Yan G100 za su yi duba da ka’idojin takara da hukuncin kotun koli a kan dokar zabe kafin su kai ga yanke hukunci.

Source: Getty Images
An dankaro wa Atiku Abubakar tambayoyi
Dandalin Ask AA na Atiku Abubakar ya wallafa amsoshin tambayoyin da ’yan Najeriya suka yi masa kamar yadda aka ji labari.
Bincike ya nuna wasu amsoshi akalla 12 cikin 100 ba su gamsar ba, domin sun gaza bada amsa yadda mutane su ka nema ba.
An tasa ‘dan takaran shugaban kasar ya yi bayani game da manufofinsa da shekarun da zai yi a ofis idan har jama'a sun zabe shi.
Asali: Legit.ng


