Zargin Shirin Hallaka Atiku Ya Je Amurka, Za a Kai Korafi ga Trump
- Wata kamfani da ke Amurka, mai alaƙa da Atiku Abubakar, ya yi magana kan zargin shirin kashe dan takarar shugaban kasa a ADC
- Kamfanin Von Batten-Montague-York ya ce zargin shirin kashe tsohon mataimakin shugaban ƙasa abin damuwa ne
- Sai dai kwamitin kamfen jam'iyyar APC ya fito ya yi magana tare da musanta rahotannin karya da ake yadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wani kamfanin ƙawance da ke Amurka, mai alaƙa da Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan zargin shirin makirci kan dan takarar shugaban kasa a ADC.
Kamfanin ya bayyana cewa yana shirin kai batun ga gwamnatin Shugaba Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka.

Source: Twitter
Wakilin Legit Hausa ya gano wannan saƙo ne da asusun @batten_von ya wallafa a shafin X a jiya Talata 20 ga watan Oktobar 2026.
Hankula sun tashi kan zarge-zargen kashe Atiku
Kamfanin ya bayyana rahotannin da ke zargin fadar shugaban Najeriya da ƙulla makircin kashe tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin abin tayar da hankali.
Saƙon ya ce:
“Dr. Von Batten yana da cikakken niyyar kai waɗannan sabbin zarge-zarge kan Shugaban Najeriya Bola Tinubu ga gwamnatin Trump da Majalisar Dokokin Amurka.”
Kamfanin ya kuma yi gargaɗin cewa za a iya samun sakamakon diflomasiyya idan aka samu kisan wani ɗan siyasa.
Lamarin dai ya jawo maganganu a tsakanin yan Najeriya inda mafi yawan mutane ke fargabar komai na iya faruwa duba da yadda siyasa ke kara zafi tsakanin yan adawa da jam'iyyun adawa.
Kyakkyawar alakar kamfanin da Atiku
Kamfanin ƙawance mai suna Von Batten-Montague-York, L.C., ya taɓa kasancewa yana da alaƙa da Atiku Abubakar, kamar yadda wani bayanin hulɗar neman tasiri da aka gabatar wa gwamnatin Amurka ya nuna.
A cewar takardun da aka shigar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, an ɗauki kamfanin aiki bisa yarjejeniyar da ake cewa ta kai dala miliyan 1.2 a shekara domin samar da shawarwari kan hulɗar gwamnati da dabarun siyasa.
Saƙon ya kuma ambaci wani aikin da ake zargin ya kai dala miliyan tara a Washington da kuma albarkatun ma’adinai na dala biliyan 700, ba tare da gabatar da takardun da za su tabbatar da waɗannan alkaluma ba.
Babu tabbacin cewa kamfanin ya miƙa zargin shirin kisan ga gwamnatin Trump ko Majalisar Dokokin Amurka a hukumance, ko kuma ɗaya daga cikinsu ya fara bincike kan lamarin.
APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku
An ji cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya yi magana kan zargin cewa akwai shirin kashe Atiku Abubakar.
APC ta buƙaci Timi Frank ya gabatar da hujjoji kan zargin, tare da kira ga hukumomin tsaro su gayyace shi domin gudanar da bincike.
Timi Frank ya nemi Donald Trump da sauran shugabannin ƙasashen duniya su sa baki kan zargin yunƙurin tsoratarwa da kama Atiku.
Asali: Legit.ng

