Al'ajabi: Wata mata ta fara aman N500 bayan dan damfara ya yi tsafi da ita

Al'ajabi: Wata mata ta fara aman N500 bayan dan damfara ya yi tsafi da ita

Wani abin al'ajabi ya faru a jihar Delta bayan wata mata mai suna Taiye ta fara aman sabbin N500 a garin Warri.

Wannnan abu mai ban mamaki ya faru ne da sanyin safiyar yau, Lahadi a wani ginin bene dake gefen kwanar JJC a kan hanyar Effurun zuwa Sapele a karamar hukumar Uvwie.

Majiyar Legit.ng da ta ziyarci wurin da abun ya faru da misalin karfe 7:40 na safe ta ce jama'a sun cika mamaki yayin da suke kallon matar na aman kudin bayan dan damfarar yanar gizo (Yahoo boy) ya tsafe matar.

Ko a jiya, Asabar, sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar an kama wani tsohon boka, Samuel Hunsu, mai shekaru 85, a garin Abeokuta, jihar Ogun da danyun zuciyoyin mutane.

Al'ajabi: Wata mata ta fara aman N500 bayan dan damfara ya yi tsafi da ita

Al'ajabi: Wata mata ta fara aman N500 bayan dan damfara ya yi tsafi da ita
Source: UGC

Yayin bajakolin Hunsu ga manema labarai, jami'an 'yan sanda na ofishin shiyya ta 2 dake Onikan a jihar Legas, sun ce dattijon ya amince da amfani da sassan jikin mutane domin tsafin kudi.

Sai dai, Hunsu ya ce wani mutum ne mai suna Abiodun ya kawo masa zuciyar domin a yi masa tsafin samun kudi.

DUBA WANNAN: An kama babban kwamandan kungiyar Boko Haram a Legas bayan musayar wuta

A cewar dattijo Hunsu, "Abiodun ne ya kawo min zuciyar bayan ya tuntube ni domin hada masa tsafin kudi kuma na fada masa abubuwan ake bukata. Nima nayi mamakin ganinsa da zuciyar mutum. Sai da na tambaye shi inda ya samo zuciyar mutum, amma sai yace ya ciro ta ne a jikin wani barawo da aka kashe a jihar Ogun. Bayan ya tafi ne sai na adana zuciyar cikin wasu sinadarai don kar ta lalace, har zuwa lokacin da zai dawo. Ban san Abiodun ba kuma ban san inda yake da zama ba. Ni dai kawai ya ce min ya zo wurina ne tun daga jihar Kwara."

Sai dai jami'an 'yan sanda ta ce sun samu rahoton cewar mutane biyu sun mutu a sansanin matsafin

A cewar 'yan sanda: "da muka tambaye shi a kan mutanen da suka mutu a sansaninsa na tsafi, sai ya ce sun mutu ne yayin zaman jinya kuma ya binne su ba tare da mayar da su ga iyalinsu ba. Bayan mun samo izinin bincike daga kotu ne muka gano zuciyoyin mutane a cikin wata roba kuma bincike ya nuna mana cewar zuciyoyin sun samu tsawon sati biyu a ajiye cikin robar."

Lawal Shehu, mataimakin babban sifeton rundunar 'yan sanda mai kula da shiyya ta 2, ya ce a ranar 17 ga watan Disamba ne suka samu rahoton cewar wani matsafi Samuel Hunsu na dauke da sassan jikin mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel