Na Kusa da Ganduje Ya Yi Tsiya, Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar APC a Kano
- Tsohon kwamishina s mulkin Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga APC, yana mai nuna damuwa kan yadda al’amuran jam’iyyar ke tabarbarewa
- Dan siyasar wanda ke kusa da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yana neman wata jam’iyya domin inganta rayuwar al’umma da ci gaban Najeriya
- Murabus ɗinsa ya zo mako guda bayan tsohon shugaban hukumar NPA, Aminu Dabo, ya fice daga APC, lamarin da ya ƙara jawo hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani tsohon kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Kano, Injiniya Mansur Ahmed, ya yi murabus daga jam’iyyar APC.
Majiyoyi suka ce ya yi murabus saboda damuwarsa kan yadda al’amuran jam’iyyar ke tabarbarewa.

Source: Facebook
Ahmed, wanda ke kusa da tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da matakin nasa ne ta hanyar wasiƙar murabus da ya miƙa wa shugaban APC na unguwar Yakasai, a ƙaramar hukumar Kano Municipal, cewar Daily Trust.
Murabus ɗinsa ya zo ne ƙasa da mako guda bayan wani fitaccen ɗan siyasa a jihar, Injiniya Aminu Dabo, tsohon manajan darakta na hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), shi ma ya fice daga jam’iyyar mai mulki.
A cikin wasiƙarsa, Ahmed ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nazari na bai ɗaya da shi da abokan siyasarsa suka yi kan halin da APC ke ciki.
Ya ce wannan yanayi, tare da buƙatar bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban jihar Kano da Najeriya, sun sa ya yanke shawarar neman wata jam’iyyar siyasa.
A cewarsa, akwai buƙatar samun wata jam’iyya da za ta ba da fifiko ga kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da inganta jin daɗin al’umma.

Source: Original
Sai dai tsohon kwamishinan ya nuna godiyarsa ga shugabanni, masu ruwa da tsaki da mambobin APC, musamman waɗanda ke Kano Municipal, bisa damar da suka ba shi na yin hidima da bayar da gudummawa ga ci gaban jam’iyyar a lokacin da yake cikinta.
Ahmed ya yi aiki a matsayin kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tsakanin shekarar 1999 da 2003.
Ya kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da kuma Jami’ar Bradford da ke Ingila.
Injiniyan ya taɓa neman takarar gwamnan Kano, sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin mai kula da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jonathan/Sambo a jihar Kano.
Ganduje ya ce Tinubu dan Kano ne
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gode wa ’yan Kannywood da suka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.
Ganduje ya bukaci ƙungiyar Triple-R ta tsaya kan adalci, gaskiya da haɗa kan al’umma yayin da take neman goyon bayan Tinubu a 2027.
Ya kuma yi kira da a ƙara zuba jari a masana’antar nishaɗin Najeriya ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da horar da matasa masu tasowa.
Asali: Legit.ng

