Kasar Ghana ta kifar da Najeriya a gasar iya dafa shinkafa dafa-duka

Kasar Ghana ta kifar da Najeriya a gasar iya dafa shinkafa dafa-duka

A wani rahoto mai kama da al'mara da muka kalato a jaridar BBC Hausa, mun samu cewa kasar Ghana ta yi kuli-kulin kubura da kasar Najeriya a gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar a dandalin taro na Cressal Park da ke birnin Accra.

Rahoton dai ya bayyana cewa, kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka inda ta yi wa kasar Najeriya dauka daya.

Wata mata da ake kira Madam Sika, ita ce ta lashe wannan gasa inda ta samu kyautar zunzurutun kudi na wuri na gugar wuri har dalar Amurka dubu biyu.

Babu shakka shinkafa dafa-duka wadda a turance ake kira "Jollof Rice", wani nau'in abinci ne mai farin jini da ya shahara a kasashen nahiyyar Afirka da dama.

KARANTA KUMA: Rikicin Tibi da Jukun: An babbake gidaje 300 a Taraba

An dai shafe tsawon lokaci musamman a dandalan sada zumunta ana adawa ta raha tsakanin Najeriya da Ghana a kan wai wace kasa ce a cikinsu shinkafa dafa-dukarta ta fi dadi.

Mun samu cewa, baya ga fatan dorewar makamancin wannan lamari a nan gaba, wadanda suka shirya gasar sun ce sun yi hakan ne domin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel