Kuma dai: An kara samun girgizar kasa a Abuja

Kuma dai: An kara samun girgizar kasa a Abuja

- A yau, Alhamis, hukumar NGSA ta tabbatar da samun wata girgizar kasa maras karfi a yankin titin Panama da ke unguwar Maitama a Abuja

- A jawabin da Dakta Abdulrazaq Garba da Vincent Owan su ka fitar a madadin hukumar NGSA, sun bayyana cewar an samu girgizar kasar ne da misalin karfe 12:45 na ranar yau

- Rahoton ya bayyana cewar tuni hukumar NGSA ta aika tura tawagar kwararru zuwa wurin domin tattara bayanai a kan afkuwar al'amarin

A yau, Alhamis, ne hukumar kula da muhalli da bayar da agajin gaggawa ta Abuja (NGSA) ta tabbatar da samun wata girgizar kasa maras karfi a yankin titin Panama da ke unguwar Maitama a Abuja.

A jawabin da Dakta Abdulrazaq Garba da Vincent Owan su ka fitar a madadin hukumar NGSA, sun bayyana cewar an samu girgizar kasar ne da misalin karfe 12:45 na ranar yau Alhamis, 01 ga watan Nuwamba, 2018.

Kuma dai: An kara samun girgizar kasa a Abuja

An kara samun girgizar kasa a Abuja
Source: Depositphotos

Rahoton ya bayyana cewar tuni hukumar NGSA ta aika tura tawagar kwararru zuwa wurin domin tattara bayanai a kan afkuwar al'amarin.

DUBA WANNAN: Hotunan makaman da aka kama 'yan Shi'a da su a Abuja

Ko a watan Oktoba sai da aka samu wata girgizar kasar a yankin Mpape da ke cikin garin Abuja. Sai dai hukuma ta alakanta afkuwar girgizar kasar da aiyukan harkar ma'adanai.

Hukumar NGSA ta ce tuni ta sanar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) tare da yin kira ga jama'a da kada su firgita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel