Ma’aurata sun fado daga tagar bene mai hawa 9 yayinda suke tarawa da junansu

Ma’aurata sun fado daga tagar bene mai hawa 9 yayinda suke tarawa da junansu

Wata mata ta mutu bayan ta fado daga saman bene mai hawa tara a kasar Rasha yayinda suke cikin jima’i, sai dai abokin harkar nata ya tsira bayan ya fadi a saman ta.

An tarar da matar mai shekara 30 babu rai a kasan gidansu da ke St Petersburg a daren ranar 5 ga watan Yuli bayan faruwar lamarin.

Idon shaida sun bayyana cewa, sun ga an jeho talbijin ta tagar dakinsu, inda daga bisani matar da mijinta mai shekara 29 suka fado kasa.

Kan matar ya bugu da kasa bayan sun fado sannan a take ta mutu, amma namijin ya tsira bayan ya fada a kanta da ciyayin da ke gefe.

Shaidu sun bayyana wa manema labarai na kasar cewa daga bisani sai mutumin ya tashi sannan ya koma wajen rawar da ake yi.

An kira yan sanda, sannan a lokacin da suka isa wajen sai masu rawan suka dunga jefarsu ta tagogin.

Rahotannin farko sun nuna cewa talbijin din ne ya kashe matar, amma hotuna daga wajen da lamarin ya afku ya nuna ta tsirara daga kugu zuwa kasa.

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Labarin wani gurgu da ya samu mukami a ofishin Shugaban Majalisa

Bayan an tambayi shaidu, masu bincike sun yanke shawarar cewa ma’auratan sun fado ta taga ne a lokacin da suke tarayya da junansu ta fannin auratayya.

Maza biyu na a bangaren lokacin da abun ya afku, amma basu da hannu a ciki.

An kaddamar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel