Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa

Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa

- Tarihi ya nuna cewar a wasu shekaru da su ka wuce, matar sarkin Machina ta haifi'yan tagwaye, mutum da maciji

- An ce wannan shine dalilin da ya sa har yanzu macizai ke da daraja a garin Machina domin ba a kashe su, kasancewar ana yi ma su kallon jinin sarauta

- Mazauna garin Machina sun yi imanin cewar macijin da aka haifa tare da sarkin garin ne ya haifi macizan da ake gani na shawagi a fadar sarki da kewaye

Duk da kasancewar jama'a da dama na ganin maciji a matsayin abin tsoro, sai ga shi a garin Machina da ke jihar Yobe macizai sun zama 'yan gida don kuwa har gaisuwa su ke kaiwa sarkin garin a fadar sa.

Tarihi ya nuna cewar a wasu shekaru da su ka wuce, matar sarkin Machina ta haifi'yan tagwaye, mutum da maciji.

Kasancewar maciji ba zai iya zama cikin mutane ba, sai macijin da aka haifa ya sulale ya koma wani tsauni da ke bayan fadar sarkin Machina.

Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa
Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa
Asali: Twitter

An ce wannan shine dalilin da ya sa har yanzu macizai ke da daraja a garin Machina domin ba a kashe su, kasancewar ana yi ma su kallon jinin sarauta.

DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Mazauna garin Machina sun yi imanin cewar macijin da aka haifa tare da sarkin garin ne ya haifi macizan da ake gani na shawagi a fadar sarki da kewaye.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan wannan rahoto, sarkin garin Machina, Dakta Bashir Albishir Bukar, ya bayyana cewar macijin da ya koma kan dutse na yin rayuwar sa da iyalinsa, kamar yadda mutane ke rayuwa a gidaje da iyalinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel