'Dan Tsohon Gwamnan Arewa Ya Rasu bayan Ya Fito daga Masallaci, An Ji Abin da Ya Faru

'Dan Tsohon Gwamnan Arewa Ya Rasu bayan Ya Fito daga Masallaci, An Ji Abin da Ya Faru

  • Arc. Shettima Muhammad Kashim, ɗan marigayi Sir Kashim Ibrahim, gwamnan farko a tsohuwar jihar Arewacin Najeriya, ya rasu a hatsarin mota a Abuja
  • Marigayin mai shekara 67 ya rasu ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, sa’o’i kaɗan bayan halartar ƙaddamar da wani littafi da ya yi nazari kan gwamnatin Tinubu
  • Abokansa sun bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, fara’a da riƙon amana wanda bai bari bambancin siyasa ya lalata alaƙarsa da mutane ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Arc. Shettima Muhammad Kashim, ɗan marigayi Sir Kashim Ibrahim, gwamnan farko ɗan asalin Arewa a tsohuwar Arewacin Najeriya, ya rasu a wani hatsarin mota a Abuja.

An ruwaito cewa Shettima, mai shekara 67, ya rasu ne ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, sa’o’i kaɗan bayan halartar ƙaddamar da wani littafi da ya yi nazari kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

Shettima Muhammad Kashim.
Shettima Muhammad Kashim, ɗan marigayi Sir Kashim Ibrahim Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Daily Trust ta ce an birne gawarsa a makabartar Gudu da ke Abuja ranar Asabar, bisa tsarin addinin Musulunci. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, na cikin ɗimbin mutanen da suka halarta.

Ya halarci taron kaddamar da littafi

An ce Shettima Muhammad ya rasu ne bayan motarsa ta yi karo da wata babbar mota da ke tsaye a yankin Asokoro na Babban Birnin Tarayya, lamarin da ya jawo masa munanan raunukan kai da suka yi sanadin mutuwarsa.

Rasuwarsa ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan ya haɗu da abokai da abokan hulɗarsa a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, domin halartar ƙaddamar da littafi kan gwamnatin Tinubu.

Daga cikin waɗanda suka yi ta’aziyya gare shi akwai Dakta Garba Abari, tsohon Shugaban Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), da Farfesa Usman Yusuf, tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS).

Abin da ya faru kafin hatsarin

Kara karanta wannan

Ajali ya gitta: Shugaban hukumar BASHCMA da 'ya'yasa 4 sun rasu lokaci 1

Abari ya ce ya shafe sa’o’i da dama tare da marigayin ranar Juma’a kafin ya tafi sallar Juma’a, ba tare da sanin cewa haɗuwarsu ce ta ƙarshe ba.

“Muna tare da shi, da wani babban abokinsa na kut da kut, Farfesa Usman Yusuf, da kuma wani abokinmu, Kwamared Kalli Gazali," in ji shim

Ya bayyana cewa sun kasance tare tun misalin ƙarfe 10:00 na safe har zuwa bayan ƙarfe 1:00 na rana a cibiyar Yar’Adua, inda suka yi raha tare da tattauna batutuwa cikin yanayin abota kamar yadda suka saba.

Abari ya ce ya bar wurin domin zuwa sallar Juma’a a Masallacin Banex, yayin da Kashim da sauran abokansa suka tafi Masallacin Juma’a na Maitama, wanda aka fi sani da Masallacin Yar’Adua.

Kashim ya rasu bayan sallar Juma'a

A cewarsa, daga baya Kashim ya kai abokansa gidajensu bayan sun idar da sallah tare da cin abincin rana, sannan ya nufi gidansa da ke Asokoro, inda hatsarin da ya yi sanadin mutuwarsa ya faru.

Abari ya ce labarin rasuwar Kashim ya ba shi mamaki matuƙa, domin an san marigayin da taka-tsantsan sosai wajen tuƙi.

Kara karanta wannan

Abin da ya fi firgita Kashim Shettima kan zaben 2027 fiye da Atiku da Obi

Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a wurin sallar jana'izar Shettima Muhammad Kashim Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook
“Shi mutum ne da ya zama abin koyi wajen tawali’u, bai taɓa nuna isa ko ɗagawa saboda irin dangin da ya fito daga cikinsu ba," in ji shi.

Abari ya ƙara da cewa duk da cewa Kashim ya fito daga iyali mai tasiri a siyasa kuma yana da nasa ra’ayoyin siyasa, bai taɓa bari bambancin ra’ayi ya lalata alaƙarsa da wasu mutane ba.

Shugaban BASHCMA ya rasu a hatsarin mota

Kun ji cewa Alhaji Ibrahim Ladan Duguri, shugaban hukumar kula da tsarin inshorar lafiya ta jihar Bauchi (BASHCMA), ya rasu tare da ’ya’yansa huɗu a hatsarin mota.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed , wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan wannan rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262