Abun Al Ajabi
Za ku ji cewa wani babban lakcara na Kwalejin Ilimi ta garin Ugbokola, Andrewa Ogbuja dan shekara 51, ya gurfana gaban kuliya bisa aikata mummunan laifi na keta haddin wata budurwa da ke masa hidimar aikace-aikacen gida.
Mun samu rahoton cewa, matafiya dake bibiyar babbar hanyar Abuja zuwa garin Keffi sun tagayyara a daren ranar Litinin din da ta gabata sakamakon aukuwar wani mummunan hatsari ya hadar da kimanin motoci 15 daban-daban.
Cikin kwaranyar hawaye ta dubunnan mutane, anyi jana'izar yara kimanin 40 da ajali ya katse masu hanzari yayin da mayakan kasar Saudiya suka kai wani mummunan hari kan wata mota dauke da al'umma a Arewacin Kasar Yemen.
Da sanadin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wani Mutum farat daya ya yi amfai d harsashi na bindiga wajen harbe 'yan uwan sa takwas da ya hadar har da kananan yara biyu kuma ya arce kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
Mista Olusegun Martins shugaban hukumar kula da tsaron manyan hanyoyi, shine ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ya ce akwai kimanin mutane biyu da suka jikkata.
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Neja ta daƙume wani ɗan acaɓa God'stime Okone, bisa laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 11 fyaɗe a yankin karamar hukumar Gurara ta jihar.
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wani Mahaifi dan shekara 45 da yake zaman daduro da diyarsa da lamarin mai cike da takaici da ya kai ga dankara ma ta juna biyu.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, mun samu rahoton cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne wani babban ma'aikacin karamar hukuma, Michael Kayode Bamisaye, ya sheke kansa murus har lahira a gidan sa dake birnin Ado Ekiti.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, wani jariri dan watanni 3 da haihuwa ya riga mu gidan gaskiya cikin wata Mota yayin da Mahaifiyar sa ta manta da shi wajen kuskuren ajiye sa a gidan raino.
Abun Al Ajabi
Samu kari