Hatsari ya salwantar rayukan Abokanai da Waliyan Ango 9 a jihar Nasarawa

Hatsari ya salwantar rayukan Abokanai da Waliyan Ango 9 a jihar Nasarawa

- Wani Mummunan hatsari ya salwantar da rayuwar Abokanai da Waliyan Ango a jihar Nasarawa

- Amaryar Angon ta kasance diya ga tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Abubakar Sodangi

- Bayan daura auren an kuma gudanar da Jana'izar mamatan da suka riga mu gidan gaskiya

Kimanin rayukan Mutane 9 sun salwanta a sanadiyar wani mummunan hatsari da ya auku a ranar Asabar din da ta gabata kan babbar hanyar garin Keffi zuwa birnin Nasarawa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wadanda ajali ya katsewa hanzari sun hadar da abokanai da Waliyan wani Ango yayin da suke kan hanyar su ta zuwa daurin aure daga jihar Zamfara zuwa Nasarawa.

Karar kwana da ba ta jinkiri ta yashe Mutane 9 nan take jim kadan bayan shigar su jihar Nasarawa da misalin karfe 10.00 na safiya domin halartar daurin auren da aka kayyade gudanar sa da misalin karfe 11.00 na safiyar wannan rana ta Asabar, 16 ga watan Dasumba.

Hatsari ya salwantar rayukan Abokanai da Waliyan Ango 9 a jihar Nasarawa

Hatsari ya salwantar rayukan Abokanai da Waliyan Ango 9 a jihar Nasarawa
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Amarya Angon ta kasance diya ga tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Abubakar Sodangi. An yi jinkiri na sa'a guda gabanin daura auren sakamakon aukuwar kaddarar da ta rigayi fata.

Babban limamin masallacin Juma'a na Marahbin shi ya kasance waliyin angon bayan rasuwar waliyin sa na asali. An gudanar da jana'izar mamatan da misalin karfe 5.00 na yammacin wannan rana da ta kasance ta murna da kuma kishiyar hakan.

KARANTA KUMA: Samari 3 sun yiwa Budurwa 'yar 18 fyade a jihar Legas

Binciken jami'an hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC, sun tabbatar a musabbabin aukuwar hatsarin da ta kasance fitar kafa guda ta Motar tawagar angon kirar Hummer Bus da ba bu makawa mai aukuwar ta auku.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Makiyaya na Fulani ta Miyetti Allah, ta bayyana cewa, 'yan siyasar kasar nan ke da alhakin rura wutar rikicin Makiyaya da Manoma a fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel