Matawalle Ya Yi Abin Alheri ga Ƴan Majalisun da Suka Dawo APC a Zamfara

Matawalle Ya Yi Abin Alheri ga Ƴan Majalisun da Suka Dawo APC a Zamfara

  • Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bai wa ’yan majalisar dokokin Zamfara takwas da suka koma APC motoci
  • ’Yan majalisar sun gode wa Matawalle bisa tallafin, tare da alƙawarin yin aiki tukuru domin marawa Bola Tinubu baya
  • Dattawan APC sun yaba wa Tinubu da Matawalle kan sulhunta ’yan jam’iyyar, amma sun buƙaci a magance sauran ƙorafe-ƙorafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Ministan Ƙasa na Tsaro, Bello Matawalle, ya bai wa wasu ’yan majalisar dokokin Zamfara takwas motoci bayan sun koma jam’iyyar APC.

’Yan majalisar sun koma APC ne a wani mataki na ƙarfafa jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Yan majalisar Zamfara da suka dawo APC
Yan Majalisar dokokin Zamfara 8 tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Matawalle ya ba yan majalisa motoci

An bayar da motocin ne domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri, taimaka musu wajen komawa Zamfara da gudanar da ayyukan siyasa a mazabunsu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

"Babu zagi": Yari ya fadi abin da za su tallata Shugaba Tinubu da shi

Wannan mataki ya zo ne yayin da shugabannin APC ke ƙoƙarin sulhunta ’yan jam’iyyar da ba su gamsu ba, domin ƙarfafa tsarin siyasar jam’iyyar a Zamfara gabanin zaɓen 2027.

An ruwaito cewa Matawalle, tsohon gwamnan Zamfara, ya bayar da umarnin sakin motocin nan take bayan wani umarni da aka ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar.

Rahotanni sun ce Tinubu ya buƙaci ’yan majalisar su koma Zamfara, su kuma yi aiki domin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar.

Yayin miƙa motocin a Gusau ranar Laraba, Manajan Daraktan Hukumar Inshorar Noma ta Najeriya, Yazid Danfulani, ya ce tallafin ya nuna yadda Matawalle ke ƙoƙarin samar da sulhu da haɗin kai a jam’iyyar.

Danfulani ya bayyana cewa ministan ya ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a APC domin inganta fahimtar juna, haɗin gwiwa da zaman lafiya tsakanin ’yan jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa bayar da motocin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa sulhu, sake haɗa ’yan majalisar da al’ummominsu da kuma inganta tattara goyon bayan jama’a a matakin ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalilin da ya sa 'yan majalisa 8 suka je wurin Tinubu bayan sun fice daga APC

Yan majalisar Zamfara sun samu motoci daga Matawalle
Taswirar jihar Zamfara da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan majalisar sun yi godiya ga Matawalle

Da yake magana a madadin takwarorinsa, Aliyu Kagara ya gode wa Matawalle bisa tallafin, tare da alƙawarin goyon bayan ƙoƙarin sake zaɓen Tinubu.

Kagara ya ce:

“Muna matuƙar godiya ga Ministan Ƙasa na Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, bisa wannan tallafi. Muna tabbatar masa da ƙudurinmu na yin aiki tuƙuru domin ganin Shugaba Bola Tinubu ya samu nasara a babban zaɓen 2027.”

Bayar da motocin ya biyo bayan yabon da Ƙungiyar Dattawan APC ta Arewa ta yi wa Tinubu da Matawalle kwanan nan.

Ƙungiyar ta yaba musu kan rawar da suka taka wajen ganin ’yan majalisar takwas sun koma jam’iyyar mai mulki.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yusuf Abubakar, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin muhimmin mataki na warware saɓanin cikin gida da sake gina haɗin kai a APC.

Abubakar ya ce:

"Muna yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa rawar da ya taka ta uba da kuma jajircewarsa wajen inganta sulhu a jam’iyyar, duk da yawan ayyukan da ke gabansa.

Kara karanta wannan

Sanata Tambuwal na shirin ficewa daga ADC zuwa APC? An ji yadda zancen yake

Yan majalisa 8 sun gana da Tinubu

Kun ji cewa ’yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar sun bayyana dalilin ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu.

Sun ce sun tattauna da shugaban ƙasar kan dakatarwar da suka bayyana a matsayin matakin da ya saba wa doka.

Ministan tsaro na ƙasa, Bello Matawalle, ne ya jagorance su zuwa wajen shugaban ƙasar domin shawo kan rikicin siyasar APC a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.