Abun Al Ajabi
Mun samu rahoton cewa wata Mata, Asma'u Shehu da 'ya'yanta 4, Yusuf, Umma, Hadi da kuma Rabi'at, sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyar aukuwar wani mummunan tsautsayi na wutar lantarki cikin unguwar Sarkin Hausawa dake jihar Neja.
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa aukuwar wani hatsarin jirgin kasa ta yi matukar muni a babban birnin Rabat na kasar Morocco dake Arewacin nahiyyar Afirka da rayukan mutane 6 suka salwanta.
Da sanadin shafin jaridar Wuzup Nigeria mun samu rahoton cewa, wani Malamin Addini ya na zargin Matar sa, Barakat Adeniyi da keta ma sa haddi inda ya nemi kotu ta shiga tsakanin auren su bayan shekaru biyu da rabi da kulla shi.
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wani Matashi ya shiga hannun hukumar 'yan sanda da laifin garkuwa da Mahaifiyar Budurwar sa a karamar hukumar Ukwa ta jihar Abia dake Kudancin Najeriya.
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, wani Mutum Isah Sulaiman, ya gurfana gaban wata Kotun Shari'a ta Magaji gari dake jihar Kaduna tare da surukarsa kan dambarwar gadon Matarsa da ta riga mu gidan gaskiya.
Da sanadin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, an tabbatar da salwantar rayuwar wani sojan kasa yayin da wasu 'yan tadda rike da bindigu suka samu nasarar yin garkuwa da wata Matashiya, Hafsat Gambo, mai shekaru 21 a duniya.
Wata babbar Kotun Majistire dake zamanta a babban birnin Minna na jihar Neja, ta bayar da umarnin garkame wani Dattijo a gidan kaso, Michael Itang mai shekaru 55 a duniya, bisa laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 10 fyade.
Kwanaki kadan da suka shude mun samu cewa wani karamin ma'aikacin sojan kasa, Anajo Aloygius na barikin Soji ta Mogadishi a babban birnin kasar nan na tarayya, ya amsa laifinsa na cin zarafin wata Mata mai Tireda a kasuwar Nyanya.
Mun samu wani rahoto na ban al'ajabi dangane da yadda wasu gungun 'yan fashi da makami da suka yiwa wani Sufeton 'yan sanda kwanton bauna, Ebri Ogban, inda suka kar shi har lahira ta hanyar harbi da harsashi na bindiga.
Abun Al Ajabi
Samu kari