'Yan Bindiga Sun Kai Harin da Ya Ritsa da Jariri da Wasu Mutane a Kaduna
- An yi zargin sace mutum biyar, ciki har da jariri mai kimanin wata guda, a Mararaban Kajuru da ke ƙaramar hukumar Kajuru
- Rahoton tsaro na al’umma ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026
- Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Kaduna da ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar ba su fitar da sanarwar jama’a kan lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - An yi zargin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyar, ciki har da jariri mai kimanin wata guda a jihar Kaduna.
'Yan bindigan dauke da makamai sun sace mutanen ne a Mararaban Kajuru, da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Source: Original
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Talata, 20 ga Oktoba, 2026, a yankin Mararaban Kajuru da ke gundumar Kufana.
Rahoton tsaro ya tabbatar da sace mutanen
Wani saƙon bayanin halin tsaro da ake yaɗawa a cikin al’umma ya bayyana cewa an sace mutanen ne a yankin da daren ranar Talata.
Saƙon ya ce:
“Wannan saƙo ne domin sanar da mu halin tsaro a Mararaban Kajuru da sanyin safiyar yau, Talata, 20 ga watan Oktoban 2026."
“Da misalin ƙarfe 1:00 na dare, a Mararaban Kajuru da ke gundumar Kufana, ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, an tabbatar da sace mutum biyar, ciki har da jariri mai wata guda, a safiyar yau.”
Saƙon ya kuma yi kira ga al’umma da su yi addu’ar ganin waɗanda aka sace sun dawo gida lafiya.
Ba a bayyana sunayen waɗanda aka sace ba
Sai dai bayanin da ake yaɗawa bai bayyana yadda sace mutanen ya faru dalla-dalla ba, haka kuma ba a bayyana sunayen waɗanda aka sace ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Hare-haren 'yan bindiga dai na zama babbar barazana ga al'umma wadanda ake kashe wa da sace wa domin samun kudin fansa.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe jami'in NSCDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), tare da yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a garin Pushit da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan ’yan bindigar sun yi garkuwa da ɗan kasuwar, sai suka hango jami’in NSCDC yana kan hanyarsa ta zuwa wani shago domin sayen katin waya, inda suka buɗe masa wuta.
Maharan sun yi zaton jami’in, wanda yake sanye da kayan farar hula, ya nufo su ne domin hana su sace ɗan kasuwar, ba tare da sanin cewa yana tafiya ne zuwa wani wuri na daban ba.
Asali: Legit.ng

