'Yar baiwa: Wata yarinya 'yar asalin Najeriya ta kammala karatun PhD tana da shekaru 14
- Esther Okada Isa ta kasance yar Najeriya wacce ke zama a kasar Birtanya ta kuma kasance yarinya mai matukar hazaka
- Esther ta rubuta jarrabawar GCSE tana shekara 6 sannanckuma ta samu sakamako mafi kyau ko da yake mahaifiyarta wacce ta kasance kwararriya a fannin lisafi ce ta koyar da ita a gida
- Yar baiwar ta kammala karatun digiri dinta na uku wato PhD kafin ta cika shekara 14 sannan kuma tana burin mallakar banki a shekaru 15
Mutum dan baiwa kan kasance wani da ke da abubuwan ban mamaki, ko wani tarin sani mai ban al'ajabi wanda zai kai shi ga samun nasarori a matakai daban-daban, kuma Allah albarkaci Najeriya da irin wadannan mutane.
A 2015, labarin wata yar shekara 10 da ta kware a fannin lissafi, Esther Okade wacce iyayenta suka kasance yan Najeriya, ya bazu a kafofin yada labaran kasashen ketare.
A cewar rahotonni, Esther wacce ke da zama a Walsall, wani gari mai masana’antu a kasar Birtaniya, bata halarci makaranta ba a waje, illa kawai mahaifiyarta da ke koyar da ita a gida. Mahaifiyarta Omonefe Okade wacce ake kira Efe, ta kasance malamar makaranta kuma kwararriya a fannin lissafi.
An tataro cewa Esther ta taso kamar sauran yara mata tsararrakin ta, ta kasance mai son wasa da kayan wasanni irin yar-tsana da kuma yin shiga irin na Elsa dake fim din Frozen amman bayan nan ta fi tsararrakinta ta fannin karatu.
Ta fara makaranta kamar yanda tsararrakinta suka fara amman sai iyayen ta suka fuskanci yarinyar mai basira ta canja gaba daya, suka kuma yanke shawaran koyar da ita a gida.
A shekara shida ta rubuta jarrabawar lissafi na GCSE, jarabawar da yan shekara 14-16 suke rubutawa a Birtaniya ta kuma yi nasara.
Yar baiwar na son fannin lissafi sosai har ta kai ga rubuta wani littafi mai suna Yummy Algebra.
KU KARANTA KUMA: Babu wani yankin Najeriya da ke karkashin ikon yan ta’adda, inji Buratai
Ta fara karatun jami’a ne da sakamako mai kyau inda ta kasance daya daga cikin dalibai mafi kankanta a jami’an ta kuma kasance ta farko a ajinta, inda take cinye duk wata jarrabawa.
Esther tace tana son ta kammala karatun ta ne cikin shekaru biyu sannan tana son ta mallaki banki a lokacin da zata kai shekara 15 saboda tsananin son da take ma lambobi. Tayi ikirarin cewa tana son taimaka ma mutane kuma banki ce hanyar taimaka musu.
Bayan samun maki masu kyau a darussanta, zata kammala PhD dinta kafin ta kai shekara 14.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng