Tirkashi: An maka boka a kotu bayan ya damfari wata mata dake zuwa wajen shi N481,000

Tirkashi: An maka boka a kotu bayan ya damfari wata mata dake zuwa wajen shi N481,000

Wani boka mai shekara 55, Fatai Olanrewaju, wanda aka fi sani da Agbefawo ya gurfana a gaban kotun Majistare da ke zama a Oshogbo a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, bisa zargin damfarar wata mai zuwa wajensa kudi har N481,000.

An gurfanar da bokan ne a gaban mai shari’a Adijat Oloyade kan tuhume-tuhume hudu da suka hada da mallakar asirai ba bisa ka’ida ba, damfara, wankiya da kuma sata.

An tattaro cewa Fatai ya wanki Olatunji Nike wadannan makudan kudade da aka bayyana domin warkar da ita daga ani cuta da take dashi , wanda ya kasance duk damfara ne.

Dan sanda mai kara, Adeoye Kayode, yace wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 17 ga watan Oktoba, 2019, da misalin karfe 10:00am a Owode Igbona a Osogbo.

A cewarsa, laifin ya kara da sashi sections 516, 419, 383 da 213 na dokar laifi CAP 34 vol II. Na jihar Osun, 2002.

Wanda ake karan ya ki amsa laifin tuhume-tuhumen da ake masa.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu fadar shugaban kasa na amfani da motocin da aka siya shekara 20 da suka wuce – Sakataren dindindin

Lauyansa, Abayomi Alayokun yaayinda yake neman a baya da belin wanda yake karaaa, ya sha alwashin cewa wanda ake karan zai gabatar da sahihan masu tsaya masa sannan kuma cewa ba zai tsallake beli ba idan aka bashi.

Adijat Oloyade, da take yank hukunci, ta bayar da belin wanda ake karan kan N250,000.00 da adanda za su tsaya masa mutane biyu sannan ta dage karar zuwa ranar 13 ga watan Disamba, 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel