Tirkashi: An tsare wani Fasto kan satar talotalo da akuya

Tirkashi: An tsare wani Fasto kan satar talotalo da akuya

Wata kotun Majistare da ke Osogbo, jihar Osun a ranar Litinin, ta garkame wani fasto mai suna Solomon Oni Opaalade a gidan yari kan satar tolotolo da akuya sannan ya yi wa mammalakin dabbobin barazana da asiri.

Babban lauyan jihar daga ma’aikatar shari’a na jihar, Mista Adekunle Adeniyyi ya fada ma kotun cewa faston ya sace talotalo guda tara wanda kudinsu ya kai N270,000 mallakar wani Mista Oluwasegun Hammed.

Ya kara da cewar wanda ake zargin ya kuma saci akuyar N18,000 mallakar wannan mutumin dai. Yace mutumin ya aikata laifin ne a yankin Baruwa da ke Osogbo.

A cewar lauyan jihar, laifin da malamin ya aikata ya kara da sashi na 390 (9) na kundin dokar jihar Osun, 2002.

Lauyan ya cigaba da bayyana cewa an samu wanda ake zargin dauke da kayan asiri da layoyi, wanda ya kara da sashi na 213 (b) na kundin doka jiha Osun.

Adekunle ya kuma fada ma kotu cewa faston ya yi amfani da layoyin wajen yin barazana ga Mista Oluwasegun ta yadda hakan ka iya haddasa rashin zaman lafiya

Opaalade ya ki amsa laifin sannan lauyansa, Mista Taiwo Awokunle ya nema masa beli.

KU KARATA KUMA: Majalisa wakilai ta nuna rashin amincewa da sabon shirin rundunar soji na ‘operation positive identification’

Da take yanke hukunci, Misis Adijat Oloyede ta yi umurni cewa a tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Ilesha har zuwa 12 ga watan Disamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel