Jam'iyyun Adawa 3 Sun Hada Kai da APC domin Tallata Shugaba Tinubu, An Jero Sunayensu

Jam'iyyun Adawa 3 Sun Hada Kai da APC domin Tallata Shugaba Tinubu, An Jero Sunayensu

  • Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi iƙirarin cewa jam’iyyun adawa 3 sun haɗa kai da APC wajen tallata Shugaba Bola Tinubu
  • Yilwatda ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda ya yi masa bayani kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen APC
  • Shugaban APC ya ce jam’iyyar ta kammala shirye-shiryen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi iƙirarin cewa manyan jam’iyyun adawa uku sun amince za su taya su yakin neman sake zaben Bola Tinubu a 2027.

Farfesa Yilwatda ya ce jam'iyyun PDP, APGA da Accord Party, sun haɗa kai da APC wajen yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Babu zagi": Yari ya fadi abin da za su tallata Shugaba Tinubu da shi

Nentawe.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda yana sa hannu kan takadar a hedkwatar jam'iyya da ke Abuja Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Shugaban APC, Yari sun gana da Tinubu

Vanguard ta ruwaito cewa Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu.

Ya gana da Tinubu ne tare da Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC (PCC), Sanata Abdulaziz Yari.

Ya ce wannan ci gaba ya nuna yadda goyon bayan shugaban ƙasar ke ƙaruwa, yana mai cewa APC ta kammala shirye-shiryen ƙaddamar da kamfe a faɗin Najeriya a Kaduna, ranar Asabar, 24 ga Oktoba.

Jam'iyyu 3 sun hada kai da APC

Shugaban APC ya ce jam’iyyar ta samu goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa da suka taɓa kayar da ita a zaɓe, lamarin da ya bayyana a matsayin alamar faɗaɗar haɗin kan siyasa da ke kewaye da shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

“Idan ka duba abin da APC ke yi a yanzu, jam’iyyun adawa suna tare da mu. Dukkan jam’iyyun siyasa da suka taɓa kayar da mu a wani zaɓe suna tare da mu.
"PDP tana tare da mu, APGA tana tare da mu, Accord Party ma tana tare da mu. Waɗannan su ne jam’iyyun siyasa da suka taɓa kayar da mu, ban da APM, kuma duk suna tare da mu a wannan yaƙin neman zaɓe.
“Wannan yana nuna cewa duka fagen siyasar Najeriya yana tare da Mai Girma Shugaban Ƙasa, kuma wannan shi ne abin da muke yi yanzu domin tabbatar da cewa mun shirya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Kaduna,” in ji shi.
APC Yari.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda tare da daraktan yakin neman zaben shugaban kasa, Sanata Abdulaziz Yari Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Sai dai bai fayyace ko goyon bayan da ya yi iƙirarin samu ya ƙunshi amincewa a hukumance daga shugabannin kasa na waɗannan jam’iyyun adawa ba, ko kuma haɗin gwiwar siyasa ne da ya haɗa da wasu mambobi da ƙungiyoyi a cikinsu.

Yadda APC za tallata Tinubu

Kun ji cewa Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben APC, Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana cewa babu wanda za su ci mutunci a lokacin kamfen Shugaba Bola Tinubu.

Yari ya ce jam’iyyar za ta gudanar da kamfen cikin mutunci, bisa muhimman batutuwan da suka shafi ƙasa, tare da gabatar da hujjarsu ta nema wa Tinubu wa'adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262