Allah gwanin kyauta: Uwar ‘ya’ya mata 8 ta sake haihuwar maza ‘yan 4 a lokaci guda

Allah gwanin kyauta: Uwar ‘ya’ya mata 8 ta sake haihuwar maza ‘yan 4 a lokaci guda

A kwanan nan ne wata mai amfani da shafin zumunta mai suna @DrAlwaysRight, ta je shafin twitte, domin bayyana wani abun al'ajabi da ta ci karo dashi a wajen aikinta.

Likitar tayi ikirarin cewa tayi nasarar karbar haihuwar wata mata da ke da yara mata takwas, inda ta sake haihuwar yara maza yan hudu a lokaci guda.

ta bayyana cewa surukan matar sun cika da farin ciki sannan basu yi kasa a gwiwa ba wajen nuna godiya gare ta tare da rungume ta akan karban haihuwar gwarazan yaransu.

"Yanzun nan na karbi haihuwar wata mata wacce ke da yara mata 8 a baya sannan Allah a sake azurta ta da yara maza 4 a lokaci guda a yau. yanzu surukanta na nuna min kauna ta hanyar ruguma na da sumbata na," inji ta.

Likitar ta kuma nuna farin ciki akan wannan dama wanda ba kasafai ake samu ba, domin ta samu damar ganin irin wannan yanayi mai kyau, saboda aikinta.

KU KARANTA KUMA: Ali ya ga Ali: Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas

Kalli yadda ta wallafa a shafin twitter:

Da take cigaba da bayani, likitar ta bayyana cewa yana da matukar zafi kallon tashin hankali a idon uwa akan tunanin jinsin abunda take dauke dashi.

Kalli abunda ta wallafa a kasa:

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel