Ganganci: Wani mutum ya mutu yayin gasar cin kwai 50

Ganganci: Wani mutum ya mutu yayin gasar cin kwai 50

- Wani abokin Subhash Yadav ya kalubalancesa cewa ba zai iya cinye kwayaye 50 ba

- Mutumin dan asalin Jaunpur a India ya mutu ne a yayin da ya cinye kwan na 42

- An garzaya dashi asibiti bayan da ya fadi amma sa'o'i kadan yace ga garinku

Wani mutum ya mutu yayin da yayi yunkurin lamushe kwayaye har 50 a wata gasa a India. Ya fadi magashiyyan ne bayan da ya ci kwan na 42.

Subhash Yadav mai shekaru 42 a duniya ya je kasuwar Bibiganj ne a Uttar Pradesh, yankin Jaunpur tare da abokinsa inda musu ya kacame tsakaninsu, in ji 'yan sanda.

DUBA WANNAN: An karrama jaruma Fati Washa a Birtaniya

Abokan biyu sun tsaida musun nasu akan wanda ya cinye kwayaye 50 zai tashi da Rs 2,000.

Yadav yayi karbi kalubalen kuma yayi kokari don har ya cinye kwayaye 41 akan na 42 ne ya fadi kasa bai san inda kansa yake ba, kamar yadda Gulf News ta sanar.

An hanzarta kaishi asibiti ne kafin a maida shi asibitin Sanjay Gandhi inda ya mutu sa'o'i kadan bayan an kaishi.

Likitoci sun bayyana cewa, Yadav ya rasa ransa ne sakamakon matsalar da ya samu akan cin kwayayen. Har yanzu dai 'yan uwansa basu yi tsokaci akan mutuwar dan uwan nasu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel