Saudi Ta Kama Mace da Namiji Suna Alfasha a Masallaci a Makkah
- Saudi Arabia ta zartar da hukuncin kisa kan wasu ’yan Bangladesh biyu da aka samu da laifin aikata abin da hukumomi suka kira alfasha a cikin wani masallaci a Makkah
- Ofishin jakadancin Bangladesh da ke Jeddah ya ce ba a sanar da shi tun kafin zartar da hukuncin ba, lamarin da ya sa ya aika da wasiƙar diflomasiyya ga hukumomin Saudiyya
- Saudiyya ta ce an yanke wa mutanen hukuncin kisa bayan kotu ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsu da shi, amma ba ta bayyana ainihin abin da suka aikata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia – Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu da aka samu da laifin aikata abin da hukumomin ƙasar suka bayyana a matsayin alfasha a cikin wani masallaci a Makka.

Kara karanta wannan
"Ba Musulmai ba ne," Shugaban majalisa ya gano wadanda suka hana zaman lafiya a Najeriya
An zartar da hukuncin a yankin Makka, kamar yadda wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar ranar Laraba ta bayyana.

Source: Getty Images
Sunayen waɗanda aka kama
Jaridar The Daily Star ta Bangladesh ta ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta bayyana sunayen mutanen biyu da aka kashe a matsayin Nazerul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar.
A cewar ma’aikatar, jami’an tsaro sun kama mutanen biyu, inda aka gudanar da bincike kafin a gurfanar da su gaban kotun da ta dace.
Sanarwar ta ce kotun ta tabbatar da zarge-zargen da ake yi musu, sannan ta yanke musu hukuncin kisa.
An ce sun keta alfarmar masallaci
Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an yanke wa mutanen hukuncin kisa bisa tsarin ta’azir, wato hukuncin da shari’ar Musulunci ta bai wa hukuma damar ƙayyade bisa yanayin laifi.
Sanarwar ta ce girman laifin da kuma keta alfarmar lokaci da wurin da aka aikata shi ne ya sa aka yanke hukuncin. An tabbatar da hukuncin daga hukumar da ta dace kafin a fitar da umarnin masarauta na zartar da shi.
Sai dai hukumomin Saudiyya ba su bayyana ainihin abin da mutanen biyu suka aikata a cikin masallacin ba. Haka kuma, ba a bayyana sunan masallacin ko lokacin da aka kama su ba.

Source: Facebook
Bayanin ofishin jakadancin Bangladesh
Bayan zartar da hukuncin, ofishin jakadancin Bangladesh da ke Jeddah ya tuntubi hukumomin Saudiyya domin neman amincewa da faruwar lamarin a hukumance.
NDTV ta wallafa cewa wani jami’in ofishin ya shaida ta hanyar saƙon WhatsApp ranar Alhamis cewa ba a sanar da ofishin tun kafin zartar da hukuncin ba.
Jami’in ya ce ofishin ya aika da wasiƙar diflomasiyya ta musamman ga Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya, yana neman a tabbatar da lamarin a hukumance.
Akpabio ya tura jama'a Makkah
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya kare kansa daga sukar da aka yi masa kan kalaman da ya yi game da Musulmi yayin muhawara a majalisar.
Akpabio ya yi jawabi a zaman majalisar ranar Alhamis, inda ya ce ya shafe shekaru 25 yana tallafa wa Musulmi wajen gudanar da aikin hajji a Makkah.
Ya yi hakan ne bayan suka da ta biyo bayan kalamansa a ranar Talata yayin tattauna kudirin dokar hukunta wanda ya yi yunkurin kashe kan shi Najeriya.
Asali: Legit.ng
