Za'a biya mutumin da nono ya fitowa diyyar naira tiriliyan biyu

Za'a biya mutumin da nono ya fitowa diyyar naira tiriliyan biyu

Wani rahoto na ban mamaki da muka kalato a jaridar BBC Hausa ya ruwaito cewa, wata kotu a Amurka, ta umarci wani kamfanin hada mugunguna na kasar, Johnson & Johnson (J&J), da ya biya wani matashi, Nicholas Murray, diyyar dala biliyan takwas.

Kotun da ke zamanta a jihar Philadelphia ta kasar Amurka, ta umarci kamfanin J&J da ya biya diyyar wannan zunzurutun kudi da suka kai naira tiriliyan biyu, biyo bayan illar da wani maganin tabin hankali na kamfanin ya yi wa Mista Nicholas na haddasa masa tsirowar nono a kirji.

Wani alkalin kotun wanda shari'arsa daya ce cikin dubbai da ya gudanar, shi ne ya zartar da wannan hukunci da cewar sai kamfanin J&J ya biya Mista Nicholas diyya mai tsoka sanadiyar illar da wani maganin kamfanin ya yi na haddasa nonuwansa suka kara girma tare da fitowa kuru-kuru tamkar na mace mai shayarwa.

Lauyoyi sun ayyana cewa, wani kamfani mai hulda da J&J, ya fifita riba a kan marasa lafiya wajen hada kwayar cutar tabin hankali mai sunan Risperdal, wanda mista Nicholas ya rinka hadiya da zummar samun waraka.

KARANTA KUMA: Gwamna AbdulRazaq ya sake aike wa da sunayen wasu kwamishinoni 6 majalisar dokokin jihar Kwara

Duk da cewa kotun na ganin babu dace a kan hakan, kamfanin J&J ya sha alwashin daukaka kara tare da samun karin gwiwar wani farfesan nazarin doka da shari'a na jami'ar Richmond, Carl Tobias, wanda ya ce akwai yiwuwar kotun daukaka karar ta rage yawan diyyar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel