Dan Tsohon Gwamna, Mustapha Sule Lamido Ya ba da Shaida a gaban Kotu

Dan Tsohon Gwamna, Mustapha Sule Lamido Ya ba da Shaida a gaban Kotu

  • Mustapha Lamido, ɗan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya musanta zargin cin hanci da rashawa da halasta kuɗaɗen haram
  • EFCC na tuhumar Sule Lamido da ’ya’yansa biyu, Aminu da Mustapha, kan zargin halasta kuɗaɗen haram da yawansu ya kai Naira biliyan 1.35
  • Mustapha ya bayyana cewa kuɗaɗen da kamfanoninsa suka samu daga kwangilolin ƙananan ayyuka sun kasance halastattu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - Mustapha Lamido, ɗan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta zargin cin hanci da rashawa da halasta kuɗaɗen haram da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ke yi masa.

Mustapha ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da shaida a matsayin mai ba da shaida na biyar a ɓangaren masu kare kansu a shari’ar da ake yi wa mahaifinsa da ’yan’uwansa a kotu.

Kara karanta wannan

Mawakin siyasa ya watsa wa Abba Kabir kasa a ido kan saka shi a kwamitin kamfe

Mustapha Sule Lamido.
Mustapha Sule Lamido, dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Mustapha Lamido
Source: Facebook

Premium Times ta ce EFCC na tuhumar Sule Lamido da ’ya’yansa, Aminu da Mustapha, kan zargin halasta kuɗaɗen haram da yawansu ya kai Naira biliyan 1.35.

Sai dai duka waɗanda EFCC din ke tuhuma sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.

Mustapha ya kare kansa a kotu

A yayin ba da shaidarsa, Mustapha ya bayyana cewa kuɗaɗen da ya samu daga wasu ƙananan kwangiloli da kamfanin Dantata and Sawoe ya ba shi sun samo asali ne daga halastattun harkokin kasuwanci.

Ya bayyana cewa ayyukan da kamfanoninsa suka gudanar sun kasance na gaskiya, yana mai cewa kuɗaɗen da suka samu sakamakon waɗannan ayyuka ba na haram ba ne.

Mustapha ya kuma yi bayani kan wasu takardun da suka shafi harkokin kasuwancin kamfanoninsa, inda ya ce an rasa wasu bayanan kamfanin sakamakon rikicin bayan zaɓen shekarar 2011 a Kano.

A cewarsa, tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen ya yi sanadin lalacewa ko ɓacewar wasu bayanai da takardun da suka shafi ayyukan kamfanonin.

Kara karanta wannan

"Gwamma na je gidan yari"; Dangote ya fadi abin da ba zai iya rabu wa da shi ba

Kotu ta amince da takardu

A yayin zaman shari’ar, lauyan masu kare kansu ya gabatar da wasu takardu da suka shafi bayanan kasuwanci da kwangilolin da ake magana a kai.

Alƙalin kotun ya amince da takardun, inda aka karɓe su a matsayin hujjoji masu lamba 84 zuwa 88.

Waɗannan takardu za su kasance cikin hujjojin da kotun za ta yi la’akari da su yayin nazarin shari’ar da kuma tantance matsayar ɓangarorin da ke cikinta.

Bayan kammala shaidar Mustapha, lauyoyin masu kare kansu sun sanar da kotun cewa sun kammala gabatar da shaidunsu.

Sule Lamido.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido yana jawabi a taro a Dutse Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

An ɗage shari’ar zuwa 2027

Bayan kammala gabatar da shaidun wadanda, kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga Janairu, 2027, domin ɓangarorin da ke shari’ar su gabatar da bayanansu na ƙarshe a rubuce.

A wannan mataki, lauyoyin EFCC da na wadanda ake kara za su gabatar da bayanan da ke bayyana hujjojinsu da dalilan da suka sa suke ganin kotu ya kamata ta yanke hukunci a kan shari’ar.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓen 2027, Tinubu ya naɗa sababbin kwamishinoni 6 a INEC

Kotun ce za ta tantance hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar kafin yanke hukunci kan zarge-zargen da EFCC ta shigar.

Sule Lamido ya gana da Pantami

Kun ji cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da wasu ‘yan takara da manyan magoya bayansa sun ziyarci Sule Lamido a gidansa a jihar Jigawa.

Pantami ya ce ba komai ya kawo su garin Bamaina ba illa mutuntawa, karramawa da girmama Sule Lamido wanda ya yi gwamna sau biyu a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262