An Yi Babban Rashi a Najeriya, Gawar Tsohon Gwamna Ta Iso Gida domin Birne Ta

An Yi Babban Rashi a Najeriya, Gawar Tsohon Gwamna Ta Iso Gida domin Birne Ta

  • Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya karɓi gawar tsohon gwamnan jihar, Emmanuel Uduaghan, a filin jirgin saman Osubi
  • Peter Obi, Godwin Obaseki da sauran manyan ’yan siyasa sun yi alhinin rasuwar Uduaghan, tare da yabawa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Delta
  • Masu jimamin rasuwar Uduaghan sun bayyana shi a matsayin jagoran da ya haɗa kan al’umma, ya inganta zaman lafiya, lafiya, ilimi da ababen more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Warri, Delta — An kawo gawar tsohon gwamnan Delta, Emmanuel Uduaghan, jihar inda Gwamna Sheriff Oborevwori da matarsa suka tarɓe ta tare da iyalan marigayin a filin jirgin saman Osubi.

Daga bisani, Oborevwori da matarsa sun ziyarci iyalan marigayin a gidansa da ke Warri, inda suka jajanta wa matarsa, Deaconess Roli Uduaghan.

An dawo da gawar tsohon gwamna gida
Gwamna Sheriff Oborevwori da marigayi Emmnuel Uduaghan. Hoto: Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

Gwamna ya yabi gudunmawar marigayi Uduaghan

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon ɗan takarar gwamna a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ubangidansa, inda ya tuna irin goyon bayan siyasa da ya samu daga gare shi, da kuma naɗa shi ɗaya daga cikin masu ba shi shawara na musamman a shekarar 2007, cewar Vanguard.

Gwamna Oborevwori ya tuna irin gagarumar gudummawa da marigayin ya bayar lokacin da yake raye a duniya.

Ya ce:

“Ya bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban Delta, musamman gina filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Asaba. Mutum ne mai ƙarancin magana, amma mai iya bayyana ra’ayinsa sosai kuma mai natsuwa. Ya rasu, amma al’ummar Delta ba za su taɓa mantawa da shi ba.”

Ɗan marigayin, Toju, ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Litinin. Uduaghan ya rasu yana da shekara 71.

Marigayin ya mulki Delta daga shekarar 2007 zuwa 2015. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishinan lafiya da sakataren gwamnatin jihar a lokacin mulkin tsohon gwamna James Ibori.

A halin da ake ciki, ana ci gaba da bayyana jimami da jinjina ga marigayin yayin da aka fara shirye-shiryen birne shi.

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi; shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Chiedu Ebie; tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki; da ɗan takarar gwamnan NDC, Deacon Chris Iyovwaye, sun yaba da gudummawar marigayin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

Obi ya tuna gudunmawar marigayi Uduaghan
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: UGC

Obi ya tuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu

A saƙon ta’aziyyarsa, Obi ya tuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu a lokacin da suke gwamnonin jihohinsu, yana mai cewa marigayin yana ɗaukar sa kamar ƙanensa.

Obi ya ce:

“Na shiga matuƙar alhini sakamakon rasuwar babban yayana kuma ƙaunataccena, Mai Girma Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, tsohon gwamnan Delta. A duk hulɗar da muka yi, yana mu’amala da ni kamar ƙanensa.”

Ya tuna yadda suka haɗa kai wajen neman a bayar da kwangilar gina gadar Neja ta biyu, wadda ya bayyana a matsayin muhimmiyar gada wajen haɗin kan ƙasa, kasuwanci da ci gaban yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

Obi ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, gwamnatin Delta da al’ummar jihar, tare da addu’ar Allah Ya ba shi hutu na har abada, cewar Punch.

Jagoran kungiyar Afenifere ya rasu

An ji cewa Pa Reuben Famuyide Fasoranti, dattijon ƙasa kuma jagoran ƙungiyar Afenifere mai fafutukar kare al'adun Yarabawa, ya rasu yana da shekaru 100.

Kara karanta wannan

Lokacin tafiya ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya ya rasu yana da shekaru 71 a duniya

Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Talata a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a Akure.

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin dattijo mai hikima, gaskiya da sadaukar da kai wajen yi wa Jihar Ondo, ƙasar Yarabawa da Najeriya hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.