Tikashi! Kwarto ya ziyarci dakunan kwanan dalibai mata a jami’ar ABU (bidiyo)

Tikashi! Kwarto ya ziyarci dakunan kwanan dalibai mata a jami’ar ABU (bidiyo)

Idan da ranka ka sha kallo, koda dai ba sabon abu bane kama kwartaye a lokacin da suke shirin shiga dakunan kwanan dalibai mata, musamman a jami’o’i.

Hakan ce ta kasance bisa ga wani labari mai ban al’ajabi da muka samu na kama wani tsoho a lokacin da yake yunkurin shiga dakin kwanan dalibai mata.

A bisa ga wani shafin mai suna northern_hibiscuss, daya daga cikin daliban makarantar wacce ta kasance mabiya shafin ce ta turo da labarin hade da bidiyon lamarin.

Ta ce an kama tsohon ne a dakin kwanan dalibai na Ribado hall, ABU Samaru, Zaria, da misalin karfe 4:00 na tsakar dare.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnoni na ganawa a Abuja

Ga yadda ta wallafa a shafin nata: "Salam Malama! Yau kawai Saiga tsohon banza a hostel dinmu(Ribado hall, ABU Samaru, Zaria.) wlh da daddare sbd karfe hudu(04:00) batayiba aka kamashi...kuma wlh abinda ya bani haushi securities a gal's hostel wulakanta mutane sukeyi akan ID card kokai student ne bazasu barshi ya shiga ba amma saiga namiji alama ma a nan ya Kwana..."

Ga yadda rubutun ya zo tare da bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel