‘Ka da Ku Shirya Birne Ni’: Malamin Addini Ya Fadi Kalar Mutuwar da Zai Yi

‘Ka da Ku Shirya Birne Ni’: Malamin Addini Ya Fadi Kalar Mutuwar da Zai Yi

  • Fastocin Najeriya, Odumeje, ya bayyana cewa ba zai mutu kamar yadda aka saba ba, sai dai zai ɓace bayan kammala aikinsa a duniya
  • Odumeje ya gargaɗi mabiyansa da kada su shirya jana’izarsa, yana mai cewa ba za su samu gawarsa domin yi masa jana’iza ba
  • Faston ya bayyana kansa a matsayin zaki da kuma wanda aka ƙaddara zai zama tauraro, yayin da kalamansa suka tayar da kura a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Wani fasto mai tayar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, Chukwuemeka Ohanemere ya yi magana kan yadda zai mutu.

Faston da aka fi sani da Odumeje, ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta bayan bayyana cewa zai ɓace ta hanyar al’ajabi maimakon ya mutu kamar yadda aka saba.

Fasto ya tayar da hankula kan yadda zai mutu
Fitaccen malamin addinin Kirista, Chukwuemeka Odumeje. Hoto: @prophet_odumeje.
Source: Instagram

Faston ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da mabiyansa, inda ya yi ikirarin cewa ba zai mutu ba, sai dai zai ɓace idan ya kammala aikin da ya zo yi a duniya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Kamfen 2027: Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya zaɓi Kano da wasu jihohi 11 a Najeriya

Fasto ya caccaki masu goyon bayan Tinubu

Ko a kwanakin baya ma, fasto Chukwuemeka "Odumeje" Ohanaemere, ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan batun yunwa da halin da ƙasa ke ciki.

Odumeje ya yi zargin cewa masu yabon gwamnatin na yin hakan ne saboda son rai, yana mai cewa shugabanni ya kamata su yi aiki domin jama'a ba kansu ba.

Malamin ya buƙaci 'yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen hukunta shugabanni, tare da neman a riƙa bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen da aka karɓo bashi.

Abin da fasto ya fada wa mabiyansa

Odumeje ya tambayi yadda mutane za su yi bikin tunawa da shi bayan mutuwarsa, yana mai jaddada cewa ba za a samu gawarsa domin yi masa jana’izar da aka saba ba.

Ya ce:

“Ba za ku taɓa yin bikin tunawa da ni bayan na mutu ba. Wa zai je ya taka ƙafarsa a jana’izata? Kada ku shirya mini jana’iza. Ba zan taɓa mutuwa ba. Abin da zan yi kawai idan na kammala aikina shi ne in ɓace.”

Kara karanta wannan

'Na ga fuskar yarinyata,' Makahon da ya shekara 27 babu idanu ya dawo yana gani

Odumeje ya kuma bayyana kansa da kalaman nuna girman kai, inda ya kira kansa zaki da kuma mutumin da aka ƙaddara zai zama tauraro.

Fasto ya fadi yadda yake son ya mutu

A baya, mun kawo muku rahoton cewa Fasto Enoch Adeboye, shugaban cocin RCCG, ya yi bayanin cewa zai so ya mutu a ranar Lahadi da ake bauta.

A wani bidiyo a sahfin YouTube na RCCG, malamin addinin ya tuna cewa akwai wani kawunsa da ya mutu a bandaki ba tare da kowani radadi ko rashin lafiya ba.

Malamin ya yi watsi da ra’ayin cewa mutane suna mutuwa ta rashin lafiya, inda ya yi addu’ar Allah yasa shi da duk wanda ke saurarensa su mutu ba tare da radadi, cuta ko rashin lafiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.