Ana saura kwana 5 auranta ruwa ya yi awon gaba da ita (hotuna)

Ana saura kwana 5 auranta ruwa ya yi awon gaba da ita (hotuna)

Rai bakon duniya inji masu iya magana, kuma a lokacin da mutum ke nashi sai na Allah ya kasance dahir. Hakan ce ta kasance da wannan matashiya mai suna Farida. A lokacin da take gab da shiga dakin auranta sai mai afkuwar ta afku.

Kamar yadda wani dan uwanta mai suna Ahmad Husain ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce kanwar tasa ta rasa ranta ana saura kwana biyar kacal auranta.

Bisa ga bayanai dai an tattaro cewa matashiyar ta rasu ne sakamakon farawa da adaidaitar da take ciki yayi a cikin wani ruwa da ya taru.

Lamarin ya afku ne a yankin Hayin Mallam Bello da ke Kaduna, sannan kuma an tattaro cewa su uku ne a cikin adaidaitan lokacin da ruwa ya yi gaba da su.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya kar ‘yar shi har lahira bayan ya buga kanta da kasa

A wani labari na daban, mun ji cewa Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta cafke wata budurwa mai suna Deborah Nwachukwu. Ana zarginta da satar motar kirar SUV, wayoyi kirar Samsung guda biyu, agogon hannu, turare da kuma wasu kudade mallakin wani mutum da ya dauketa kwanan gida.

Lamarin ya faru ne a titin MKO, Ikeja, inda 'yan sandan suka bayyana sunan mutumin da Patrick.

Patrick ya bayyana cewa, yayi hayar Deborah ne don ta tsaftace masa gidansa da dare. Amma Deborah ta musanta hakan, ta bayyana cewa kwanan gida ya dauketa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel