Himalaya: Kabilar da basu san kishi ba, maza biyu ke auren mace daya

Himalaya: Kabilar da basu san kishi ba, maza biyu ke auren mace daya

Idan aka yi maganar aure, abinda ke zuwa zukatan mutane shine mata da miji. Wasu kan yi tunanin miji da matansa. Babu mai kawo zancen mace daya da maza da yawa a matsayin aure.

Amma kuma, a kabilar Himalayan na yankin Nepal, 'yan uwa biyu suna auren mace daya. Ana yin hakan ne don a gudu tare a tsira tare a yankin. Iyalan suna dogaro ne da karamar gona wacce a ciki ake ci da sha tare da tsare bukatun gida.

Sau da yawa matan kan auri yaya da farko, idan kanin ya kawo girma, sai ya auri matar yayan nashi kuma su dinga rayuwa a gida daya.

DUBA WANNAN: Pantami ya bayyana irin shirin da ma'aikatarsa ke yi wa matasan da suka kammala karatu

Wasu matan kan raini kannin mijin har zuwa lokacin da zasu girma su auri matan har su dinga mu'amalar auratayya, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

A irin wannan tsarin, babu zancen kishi tsakanin 'yan uwan tunda suna hakan ne don rufawa juna asiri. Hakan kuma kan zamo wata hanya ta tsarin iyali tunda mata basu cika daukar ciki ba.

Matar ta kan samu kwanciyar hankali saboda ba zata kasance cikin kadaici ba ko bayan mutuwar daya daga cikin mazan nata. Sun kuma yarda cewa, 'ya'yan da aka haifa a irin wannan auren sun fi samun kulawa ko a gaba.

Duk da kuwa cewa, wannan tsarin na mutuwa ko wancan yankin na duniya, wasu daga cikin mutanen yankin nayi don samun rufin asiri a rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel