Bariki: Budurwa ta yashe wani mutum da ya dauke ta kwanan gida, ta gudu da motarsa da wayoyi

Bariki: Budurwa ta yashe wani mutum da ya dauke ta kwanan gida, ta gudu da motarsa da wayoyi

Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta cafke wata budurwa mai suna Deborah Nwachukwu. Ana zarginta da satar motar kirar SUV, wayoyi kirar Samsung guda biyu, agogon hannu, turare da kuma wasu kudade mallakin wani mutum da ya dauketa kwanan gida.

Lamarin ya faru ne a titin MKO, Ikeja, inda 'yan sandan suka bayyana sunan mutumin da Patrick.

Patrick ya bayyana cewa, yayi hayar Deborah ne don ta tsaftace masa gidansa da dare. Amma Deborah ta musanta hakan, ta bayyana cewa kwanan gida ya dauketa.

Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan yankin, Bala Elkana ya sanar, a ranar 21 ga watan Oktoba ne hukumar tasu ta samu koken daga Patrick. Ya bayyana cewa, wacce yake zargin 'yar asalin jihar Abia ce kuma tana zaune a gida mai lamba 19, titin Irewale, yankin Ipade dake jihar legas. Ta sunkuce masa dukiyoyinsa ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Mudassir and Brothers: Dan kasuwa zai gina kamfanin atamfa na $50m a Kano

Patrick ya bayyana cewa, ya gayyaci Deborah ne don taimakawa ta tsaftace masa gidansa duk da kuwa ya hadu da ita ne a Shoprite da ke Ikeja. Sun kuma yi yarjejeniyar zai biyata N20,000 in ta kammala aikinta.

Kamar yadda 'yan sandan suka sanar, "Lokacin da aka tuhumi Deborah, ta sanar da hukumar cewa, ba tsaftace gida kadai ya gayyaceta ba. Kwanan gida suka yi yarjejeniya. bayan sun kammala masha'arsu, sai ta lura cewa nannauyan barci ya tafi da Patrick. Bata yi kasa a guiwa ba ta kwashe wayoyinsa guda biyu, agogon hannu, turare, kudade da kuma motarsa kirar SUV ta tsere dasu bayan da ta rufesa a dakin."

"Rundunar 'yan sanda masu bincike wadanda suka samu jagorancin CSP Gbenga Ogunsaki ne suka cafke wacce ake zargin tare da samo duk abubuwan da ta sata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel