Ashsha! Yaro ya rasa ransa bayan da ya kwana yana wasa a na'ura mai kwakwalwa

Ashsha! Yaro ya rasa ransa bayan da ya kwana yana wasa a na'ura mai kwakwalwa

- Wani yaro mai suna Piyawat Hariku a kasar Thailand ya hadu da ajalinsa yayin da ya kwana yana wasan bidiyo a kwamfuta

- Mahaifin ya yaron ya bayyana cewa, ya saba jan hankalin yaro akan ya rage hakan amma hakan yaci tura

- Da tsananin alhini mahaifin ke fatan mutuwar dansa ta zama darasi ga yara masu irin wannan hali

Wani yaro mai shekaru 17 a duniya ya rasa ransa bayan da ya kwana yana wasa a na’ura mai kwakwalwa.

Yaron mai suna Piyawat Harikun daga Udon Thani a kasar Thailand yana hutu ne lokacin da abun ya faru. Ya fadi ne inda ya mutu a gaban na’urar mai kwakwalwa.

Mahaifin Piyawat, Jaranwit, yace sun same shi ne ya fado daga kujerar da ke gaban na’urar mai kwakwalwa bayan da suka shiga dakinsa a ranar Litinin 5 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Na fuskanci wariyar launin fata a Bundesliga - Akpoborie

Kamar yadda mahaifin yace, “Mun samu kwanikan abinci a dakin. Ya saba zama duk dare yana wasa a na’ura mai kwakwalwa, har da rana yana yi. Yana kwashe sa’o’I masu yawa akan na’urar mai kwakwalwa yana wasa. Muna kai mishi abinci har daki tare da yi mishi Magana da ya dena amma Piyawat baya ji”.

Na kira sunanshi ina cewa ya tashi amma babu amsa. Daga fuskarshi na gane ya rasu,” in ji mahaifin.

Da na mai wayau ne kuma yana kokari a makaranta amma babbar matsalarshi it ace wasa da na’ura mai kwakwalwa. Na yi kokarin hanashi amma kullum sai yace zai rage. Amma yanzu kuwa lokaci ya kure. Ya mutu kafin ya samu damar canzawan,” in ji mahaifin Piyawat.

“Inason fatan mutuwar da na ta zamo darasi ga sauran iyayen da ke kyale yaransu suna nacewa wasa. Akwai bukatar yara su san lokacin wasa da na sauran lamurran rayuwa. Idan bah aka ba zasu kare kamar da na,” a cewar mahaifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel