Ko kadan tsoron hukuma ba shi ne dalilin da ya sanya na rufe gidan mari ba - Sheikh Muhammadu Aminu

Ko kadan tsoron hukuma ba shi ne dalilin da ya sanya na rufe gidan mari ba - Sheikh Muhammadu Aminu

Shugaban daya daga cikin shahararrun makarantun ladabtar da kangararru da ke jihar Kano, Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar, yayin wata hirarsa da manema labarai na BBC Hausa ya fadi dalilin rufe cibiyarsa ta mari.

Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar wanda ya kasance shugaban makarantar nan ta mari da ke unguwar Arzai, wadda ta fi shahara da Manzo Arzai, ya sallami dukkanin dalibansa tare da rufe makarantar da ke cikin birnin Kanon Dabo.

Lamarin na zuwa ne bayar irin dirar mikiya da rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi wa wasu makarantun mari da ke wasu sassa a Arewacin kasar nan.

Sai dai Sheikh Aminu ya labartawa manema labarai cewa, ko kodan tsoron shiga hannun jami'an tsaro bai kasance dalilin da ya sanya ya rufe makarantarsa ba a daidai wannan lokaci da gwamnatin kasar nan ke kalubantar ire-iren cibiyoyin ladabtar da wadanda suka kangare.

Shugaban makarantar Manzo Arzai ya ce "ya yi amannar ba ya muzgunawa ko azabtar da wadanda yake kula da su". Saboda haka ba ya da wata fargaba a kan irin dirar mikiyar da jami'an tsaro ke yi.

Illa iyaka ya ce ya yanke hukuncin rufe cibiyarsa ne a sanadiyar bin umarnin na gaba da shi wadanda da yawansu sun kasance iyaye kuma malamai a gare shi.

KARANTA KUMA: Dakaru sun kashe mutane biyu sanadiyar tsokanar budurwar babban soja a jihar Sakkwato

Ana iya tuna cewa, a makonnin baya-bayan nan ne hukumomin tsaro suka kai simamne wasu gidajen mari a unguwar Rigasa da ke jiha Kaduna, inda suka ceto daurarrun dalibai fiye da 100 da suka hadar har da mata.

Biyo baya sa bakin kungiyoyi masu kare hakkin bil Adama na nan gida da kuma na kasashen ketare, gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe ire-iren wadannan cibiyoyin ladabtar da kangararru da ake zargi ana keta masu haddi, wanda a wasu lokutan ma ake zargin yin lalata da su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel