Kiriniya: Wani yaro mai shekaru 8 ya faki idon iyayensa ya tuka mota ya fita tare da kaninsa mai shekaru 5

Kiriniya: Wani yaro mai shekaru 8 ya faki idon iyayensa ya tuka mota ya fita tare da kaninsa mai shekaru 5

Wani yaro dan shekara takwas tare da kaninsa mai shekara biyar sun yi hatsari da motar mahaifansu a birnin Hagen dake yankin Arewa maso yammacin Kasar Jamus, bayan sun yi tafiyar wasu yan mitoci, rundunar yan sanda kasar ta bayyana a ranar Talata.

A cewar yan sanda, babu wanda ya ji rauni a hatsarin amman motar ta bugu sosai ta yanda bata motsa ba har sai da aka ja ta.

Wasu shaidu ne suka kira yan sanda zuwa inda lamarin ya faru da misalin karfe 11:30 na dare.

A cewar yan sandan, babban mai shekara takwas din ne ya zauna a mazaunin direba sannan dan shekara 5 din ya kasance zaune a kujerar fasinja.

Babban yayi yunkurin tuka motar na wasu yan mintoci zuwa wani unguwa sannan ya sake juyawa zuwa wani wurin.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-baci a hanyoyinta

Iyayen yaran sun bayyana cewa yaran sun sulale ne ba tare da sanin kowa ba.

Yan sandan sun yi karar iyayen bisa rashin sauke hakkinsu a matsayinsu na masu kula da yara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel