Abin Mamaki: An Tsinci Gawar Magidanci da Wani Irin Rauni a Al'aurarsa, Matarsa Ta Gudu
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da gano gawar wani magidanci dan shekara 30, Haruna Ishaka a yankin karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba
- Rahotanni sun ce matar marigayin mai shekaru 24, mai suna Maimuna, ta tsere bayan faruwar lamarin, wanda ya auku da misalin ƙarfe 11:15 na dare
- Wasu majiyoyi da suka san yadda lamarin ya faru sun yi zargin cewa ma’auratan suna fama da saɓani a aurensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta fara bincike domin gano musabbabin mutuwar wani mutum mai shekaru 30, Haruna Ishaka, bayan wani rikicin cikin gida da ake zargin ya faru a ƙauyen Maigoje, ƙaramar hukumar Gashaka.
Rahotanni sun ce matar marigayin mai shekaru 24, mai suna Maimuna, ta tsere bayan faruwar lamarin, wanda ya auku da misalin ƙarfe 11:15 na daren Litinin a unguwar Mai Idanu.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama wasu matasa 2 da ba a yi tsammani ba ɗauke da bindiga a Kano

Source: Twitter
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Victor Mshelizah, ya tabbatar da cewa rundunar ta samu labarin abin da ya faru, kuma an fara ƙoƙarin gano musabbabin lamarin, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Yadda aka gano gawar mutumin
Mshelizah ya ƙara da cewa jami’in ’yan sanda mai kula da sashen yankin (DPO) yana kan hanyarsa ta zuwa wurin domin gudanar da bincike kan yanayin da mutumin ya rasu.
“An ruwaito cewa an sami Ishaka da mummunan rauni a al’aurarsa bayan rikicin da ake zargin ya faru a gidan ma’auratan. Daga bisani ya rasu a safiyar Talata.
“Ko da yake bayanan farko sun nuna cewa da yiwuwar fadan ma'auratan ne ya jawo faruwar lamarin, har yanzu ba a gano ainihin abin da ya jawo rikicin da ya yi sanadin mutuwarsa ba,” in ji Mshelizah.
Dalilin fadan ma'auratan
Wasu majiyoyi da suka san yadda lamarin ya faru sun yi zargin cewa ma’auratan suna fama da saɓani a aurensu sakamakon neman matan da ake zargin mijin yana yi.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da waɗannan zarge-zargen ta wata hanya mai zaman kanta ba, kuma ba a fayyace ko saɓanin da ake magana a kai yana da alaƙa kai tsaye da lamarin ba.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa har yanzu ba a san inda Maimuna take ba, yayin da ’yan sanda ba su fitar da ƙarin bayani kan binciken ko tabbatar da ko an kama wani mutum ba.

Source: Original
An ruwaito cewa an birne marigayin, wanda Bafillatani ne, bisa tsarin jana’izar Musulunci.
Ana sa ran binciken ’yan sanda zai fayyace jerin abubuwan da suka faru kafin mutuwar Ishaka, tare da gano yanayin da ya jawo masa raunukan da ya samu.
Magidanci ya kashe matarsa a Nasarawa
Kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama wani mutum bisa zargin dukan matarsa har ta mutu a jihar Nasarawa.
Rahotanni sun nuna cewa magidancin da ake zargi da aikata wannan danyen aiki, ya ce ya daki matar ne saboda ta ƙi dafa masa abinci.
Asali: Legit.ng
