Titunan Najeriya basa cikin mummunan hali, in ji ministan Buhari

Titunan Najeriya basa cikin mummunan hali, in ji ministan Buhari

Ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, SAN, a ranar Laraba ya jaddada cewa, titunan Najeriya basu yi lalacewar da kullum ake magana a kai ba kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Yayin da yayi magana da manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi jiya Laraba, yace ana zuzuta rashin kyan titunan Najeriya ne kawai.

Taron majalisar zartarwar da ya samu shugabancin mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, ya aminta da yin titunan Bida zuwa Sachi zuwa Nupeko da gadar Nupeko zuwa Patigi da ke kan kogin Niger, wacce ta hada Nupeko da Patigi a jihohin Niger da Kwara.

A ranar 24 ga watan Yuni, jaridar Punch ta ruwaito mummunan halin da titunan tarayya suke ciki a Najeriya. Kamar yadda rahoton ya nuna, lalacewar titunan na taka rawar gani wajen taimakawa 'yan bindiga da fulani makiyaya masu sace mutane tare da garkuwa dasu akan manyan hanyoyin.

Wasu daga cikin titunan da rahoton ya kawo sun hada da: Titi mai kilomita 110 na Gusau zuwa Dansadau da ke jihar Zamfara; titin Oyo-Iseyin dake jihar Edo da kuma titin Makurdi zuwa Gboko zuwa Katsina Ala zuwa Zaki Biam wanda ya hada jihar Benuwe da Taraba.

Amma a ranar Laraba, Fashola ya yi watsi da rahoton yadda manyan hanyoyin ke cikin mummunan hali. "Titunan basu yi lalacewar da ake fadi ba. Nasan wannan zai zamo kanun labaranku amma titunanmu ba lalatattu bane", ya sanar da manema labaran gidan gwamnati.

DUBA WANNAN: Abba Kyari ya fi Osinbajo karfin iko: 'Yan Najeriya sun mayarwa dan majalisar APC martani

Ministan ya bayyana cewa, ba don kalubalen kudi ba, da tuni an dade da kammala aiyukan titunan kasar nan.

Fashola ya kara da bayyana cewa, wasu daga cikin jihohin kasar nan suna samun ruwa mai karfi wanda hakan ne yake hana gyaran titunan ballantana lokacin damina.

Yayin maida martani ga ikirarin Fashola, shugaban kwamitin habaka ababen more rayuwa, Ibrahim Usman ya musanta abinda ministan ya fadi. Yace titunan Najeriya basu da kyau ko kadan.

Yace, "Ina tunanin ministan ya kasance mai mako yayin sanar da gaskiya. Titunan kasar nan na cikin mugun yanayi. A misali titin Biu zuwa Gombe da ake daukar sa'a daya da rabi a da wajen wucewa, yanzu sai mutum yayi sa'o'i hudu akanshi. Abu daya dai shine Boko Haram basu kanainaye titin ba. Ga titin Damaturu zuwa Biu, shima duk labarin daya ne."

Babban daraktan NECA kuwa, Timothy Olawale, yace akwai yuwuwar ministan baya bin titunan da 'yan Najeriya ke bi. Ya lissafo wasu tituna dake cikin munanan hali da suka hada da titin Ibadan zuwa Oyo zuwa Ogbomoso, Asaba da kuma Enugu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel