Tinubu na da Abin da Zai Fadawa Yan Najeriya Su Zabe Shi a 2027? Baba Ahmed Ya Yi Magana
- Shugaban jam'iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya gaza.
- Baba-Ahmed ya yi ikirarin cewa cewa shugaban ba shi da abin da zai gaya wa ’yan Najeriya domin su sake zabensa karo na biyu a zaɓen 2027
- Ya yi zargin cewa tsauraran matakan tattalin arzikin da Tinubu ya ɗauka sun cutar da talakawa maimakon inganta rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya gaza.
Ya kuma yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da wani abu da zai gaya wa ’yan Najeriya yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata.

Kara karanta wannan
"Kai ne Masar," Atiku ya maida martani bayan Tinubu ya yi misali da tarihin Annabi Musa AS
Baba-Ahmed ya soki gwamnatin Tinubu
Shugaban na PRP ya soki gwamnatin Tinubu kan tabarbarewar tsaro, matsin tattalin arziki da kuma illolin manufofinta ga ’yan Najeriya.
“Tinubu ya gaji Najeriya, amma me ya yi da ita? Ya gaji ƙasa matalauciya; ya gaji cibiyoyi marasa ƙarfi; ya gaji talauci da rashin tsaro. Ba mu zarge shi kan abin da ya gada ba, amma ya shafe shekaru uku da rabi yana mulki. Ya gaza,” in ji shi.
Ya kuma yi tambaya kan rahotannin da ke cewa shugaban ƙasar zai je yakin neman zabe a wasu wurare kaɗan ne, ba duka jihohin Najeriya ba.
Me Tinubu zai fadawa yan Najeriya?
Baba-Ahmed ya yi tambayar dalilin da zai hana Tinubu jajircewa wajen haɗuwa da ’yan Najeriya da kuma yi musu bayani kan manufofinsa da tasirinsu a rayuwarsu.
“Me ya sa Tinubu ba zai ɗauki alƙawarin cewa, ina da kuzari, ina da niyya, ina son ganin ’yan Najeriya, ina son su gan ni, ina son su ji ina bayyana musu dalilin da ya sa yunwarsu ta ƙaru?” in ji Baba-Ahmed.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba
Da aka tambaye shi dalilin da yake ganin Tinubu ba zai iya zuwa ko'ina kamfe a Najeriya ba, Baba-Ahmed ya amsa da cewa:
"Eh, ba shi da abin da zai gaya musu. Ina gaya muku, ba shi da abin da zai gaya wa ’yan Najeriya.”
Ya tabo batun yunwa da tsaro
Baba-Ahmed ya kuma soki sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin, yana mai cewa tsauraran matakan da Tinubu ya ɗauka sun cutar da talakawa maimakon inganta rayuwarsu.
Ya kuma yi tambaya kan tasirin manufofin gwamnatin ga harkar ilimi, musamman ga yaran da ke zaune a yankunan da matsalar rashin tsaro ta shafa.

Source: UGC
Shugaban PRP ya kuma yi zargin cewa matsalar rashin tsaro ta ƙara ta’azzara a ƙarƙashin gwamnatin yanzu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
“Tsaro ya tabarbare sosai. Ba a taɓa samun yanayi irin wannan na rashin tsaro ba,” in ji shi.
PRP ta gano shirin yaran Tinubu
Kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da wulaƙanta ’yan Arewa da kuma yin watsi da su.
Hakeem Baba Ahmed ya gargaɗi magoya bayan shugaban ƙasar kan yunƙurin neman ƙuri’u ta hanyar raba kuɗi a babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng