Abun Al Ajabi
Wani dattijo mai shekaru 74 ya roki kotu da ta kwato masa kudi N50,000 da ya kashe wa wata budurwa yar shekaru 18, Rukaiyyat Idris bayan an hana shi aurenta.
Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ke jego, Evelyn, a wani asibitin kudi da ke Okpoko, karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra, inda ta haifi 'yan uku.
Kamfanin motoci ta Kantanka karkashin jagorancin Shugaban kamfanonin Kantanka Group, ta kera wata sabuwar mota wanda wani matashi dan shekara 18 ya fara kerawa.
Wani bawan Allah ya shiga tsakanin wasu kaji guda biyu da ke fada, mutumin rike da kaji a dukka bangarorinsa biyu na hagu da dama yayinda yake yi masu nasiha.
Soyayya ruwan zuma dadi sannan idan ta baci ta fi madaci, hakan ce ta kasance ga likitan kasar Ghana, bayan bayyanar bidiyonsa yana ta rusa kuka kamar karamin.
An yi jana'izar malamin jami’ar Christian University of Mkar, Mkar, Gboko (UMM), Mista Moses Tarnongu, wanda tirela ta bi ta kansu tare da matarsa da yaransu 3.
Mace mai kamar maza ita ce wata matashiyar budurwa mai suna Fehintoluwa Okegbenle, ta samu wannan suna ne bayan ta tuka babur da kanta daga Lagas zuwa Abuja.
Kotu ta tsare wasu mazaje su shida, a garin Osogbo, bayan gurfanar dasu bisa zargin samunsu da gawar wani mutum, Salami Adisa da kudirin yin kudin asiri da shi.
Wata matashiya yar shekara 15 mai suna Doris, ta shafe fiye da mako guda tana fitar da kukan jini daga idanunta, lamarin da likitoci suka gaza shawo kansa.
Abun Al Ajabi
Samu kari