Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

- Kamfanin Kantanka Vehicles ta sake kera motar nan da wani dan shekaru 18, Kelvin Odartei ya kera da kayan gwangwan

- Safo Kantanka Jnr, Shugaban kamfanin kera motocin, ya wallafa hoton motar wanda ake kan kerawa sannan ya ambaci cewa za a kira ta da Akofena

- Koda dai ba a gama tabbatarwa ba, an yarda cewa kamfanin kera motoci ta Kantanka na kera sabuwar ne da hadin gwiwar matashin

Kamfanin kera motoci ta Kantanka karkashin jagorancin Shugaban kamfanonin Kantanka Group, ta kera wata sabuwar mota mai suna Kantanka Akofena.

A wani wallafa da Legit.ng ta gano a shafin Twitter na shugaban, ya wallafa wani hoto na motar wacce har yanzu ake kan aiki a kanta a kamfanin.

Motar ta Akofena, kamar yadda aka nuno a hoton, tana dauke da suffa iri guda da tsarin motar da Kelvin Odartey, matashi dan shekaru 18 da ke karamar makarantar sakandare ya kera.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Ana zargin Kwamandan Hisbah da lakume kayan tallafin korona a Kano

Kalli wallafar a kasa:

A tuna cewa wani bidiyo na matashi dan shekaru 18 da ya kammala karamar makarantar sakandare ya yi fice a soshiyal midiya a yan makonnin da suka gabata, bayan ya kera wata mota da kayan gwangwan.

Bayan nan ne matashin ya samu gurbin karatu kyauta daga wajen Kwadwo Safo Junior.

An tattaro cewa matashin wanda ya birge mutane da dama a shafin soshiyal midiya ya tuka motar da ya kera da hannunsa zuwa cibiyar rubuta jarrabawa domin rubuta jarrabawarsa ta karshe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda

Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera
Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera Hoto: @kwadwosafo_Jnr
Asali: Twitter

Koda dai ba a tabbatar ba, an yarda cewa kamfanin kera motoci ta Kantanka na kera sabuwar motar da hadin gwiwar matashin ne.

A wani labarin, wani Bawan Allah daga jihar Yobe da ya wakilci mutanen Najeriya a gasar ilmin sinadarai da aka gudanar a garin Abuja, ya samu nasara mai tarihi.

Rahotanni da-dama sun tabbatar da cewa Malam Umar Usman Dagona ya zo na daya a wannan katafaren gasa da aka shirya da kasashen Duniya.

Umar Usman Dagona ya na cikin wadanda su ka tsallaka zuwa matakin karshe na wannan gasa mai suna “Imaginechemistry" da aka yi kwanan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng