Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta

Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta

- Dattijo mai shekaru 72, ya maka wata matashiyar budurwa mai shekaru 18 a gaban kotun Gwagwalada

- Musa Abdullahi ya nemi kotu ta kwatan masa kudi N50,200 da yayi ikirarin kashewa budurwar bayan ta ki amsa tayin aurensa

- Sai dai kuma budurwar, Rukayya ta karyata ikirarin tsohon, ta ce gaba daya abunda ta san ya kashe mata shine N8,000

Wani tsohon dan shekaru 72, Musa Abdullahi, ya bukaci wata kotu da ke yankin Gwagwalada, Abuja, da ta tursasa wata budurwa yar shekaru 18, Rukayya Idris, ta biya shi kudi N50,200 da ya kashe mata tunda ta ki yarda da tayin auren da yayi mata.

Abdullahi, wanda ke zama a Baure Anguwar Hausawa a Gwagwalada, ya fada ma kotu cewa ya nemi auren Rukayya a watan Yunin 2020 sannan ta amince za ta aure shi.

Amma kuma cewa bayan wasu watanni ta karyata amsa tayin aurensa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta
Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: ‘Yan PDP za su nemi su jawo wa tazarcen Mahmud Yakubu tasgaro a Majalisa

Ya fada ma kotun cewa daga watan Yuni zuwa Nuwamban 2020, ya kashe wa matashiyar kudi N50,200 don haka ya bukaci kotu ta yi mata umurnin biyansa kudinsa.

Sai dai kuma, mahaifin yarinyar, Idris Abdullahi, wanda ya halarci kotu tare da yarsa ya karyata kudaden da mai karar yayi ikirarin kashe wa yar tasa.

Idris ya bayyana cewa shi dai abunda ya sani shine N6,000 wanda mai karar ya bashi a lokacin da ya ziyarci gidansa.

Hakazalika, matashiyar ta karyata N50,200 da mai karar yayi ikirarin kashe mata, cewa abunda ta san ya bata gaba daya shine N8,000 a lokuta mabanbanta.

KU KARANTA KUMA: Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano

Alkalin kotun, Adamu Isah, ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba, domin ba mai karar tabbatar da ikirarinsa na kashewa matashiyar N50,200.

A gefe guda, Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta kama wata yarinya 'yar shekara 19, mai suna Jemila Ibrahim da kawarta, Fatima Mohammed, mai shekaru 21 dake Monkey Village wurin Festac Area a Legas.

Ana zarginta da banka wa gidan wani Mohammed Yusuf na Monkey Village a Legas, wacce budurwarsa Rabi, take zaune a gidan, a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel