Hadimin Buhari Zai Bude Babin 2023 Ya Tona Abin da Ya Faru Lokacin Neman Takarar APC

Hadimin Buhari Zai Bude Babin 2023 Ya Tona Abin da Ya Faru Lokacin Neman Takarar APC

  • Bashir Ahmad ya bayyana cewa adadin kuria 16 da ake yayatawa cewa ya samu a zaben tsaida gwani a 2022 ba gaskiya ba ne
  • Matasahin ‘dan siyasar ya ce ba a gudanar da ingantaccen zaben fitar da gwani ba, kuma yana da shaidun magudin a bidiyo
  • A zaben 2023, Bashir Ahmad ya nemi kujerar majalisar wakilan tarayya, ya wakici mutanen Gaya/Ajingi/Albasu a inuwar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Bashir Ahmad ya yi watsi da alkaluman da mawaki Davido da magoya bayansa ke amfani da su wajen yi masa ba'a kan siyasa.

Tsohon mataimaki na musamman shugaban kasa ya musanta rahotannin da ke cewa kuria 16 kacal ya samu a zaben tsaida gwanin 2022.

Bashir Ahmad
Bashir Ahmad tare da Shugaban APC na kasa da hoton Majalisar wakilan tarayya Hoto: @BashirAhmaad/@HouseNgr
Source: Twitter

Bashir Ahmad ya sake sukar zaben gwanin APC

Da yake karin haske a shafin X da ya fi shahara da Twitter, Bashir Ahmad ya yi maganar takarar da ya so ya nema lokacin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Siyasa ta yi zafi, an bindige yaro ɗan shekara 12 yayin kamfen APC

Matashin ya yi yunkurin zama dan Majalisar wakilai, ya nemi ya samu tikitin jam'iyyar APC a shekarar 2022, amma bai iya kai labari ba.

A cewarsa, ko kadan APC ba ta yi zaben fitar da gwani na gaskiya ba a mazabarsa ta Gaya/Ajingi/Albasu da ke yankin Kudancin jihar Kano.

Kuri'a 16 Bashir Ahmad ya samu a takara?

Tun da yana ganin an yi magudi wajen tsaida ‘dan takara, ya yi watsi da kuri’u 16 da ake cewa ya samu da ya shiga zaben zama 'dan takara a lokacin.

“Ba gaskiya ba ne a ce na samu kuri’u 16. A zahirin lamari, babu zaben tsaida gwanin da aka yi tun farko.
Da an yi zabe, ina da kwarin guiwar cewa ni zan yi nasara.”

- In ji Bashir Ahmmad

Meyasa Bashir Ahmad ya dawo da maganar?

Wannan karin haske ya zama dole ne bayan sabaninsa da David Adeleke, fitaccen mawakin Najeriya da jama’a suka fi sani da Davido a dandalin X.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Mawaki Davido ya shirya kai korafi ga Donald Trump na Amurka

Bashir ya jaddada cewa yana da kwararan hujjoji, ciki har da bidiyoyi, da ke tabbatar da yadda aka tafka magudi wajen zaben 'dan takararsu na APC.

Bashir Ahmad yake cewa:

"Saboda haka duk wasu alkaluma da Davido da masoyansa ko wasu dabam suke fitarwa daga yunkurin tsaida 'dan takaran ba gaskiya ba ne.

Tsohon ‘dan jaridar ya yi alkawarin bayyana cikakken bayanin abin da ya faru a Kano lokacin da ya ajiye mukaminsa domin neman tikitin zuwa majalisa.

Daga baya Muhammadu Buhari ya maida shi kan kujerarsa, makaonni da yin murabus da nufin samun tsaya wa takarar 'dan majalisa a zaben 2023.

Bashir Ahmad ya saye fam a APC

A zaben da ya wuce, Legit ta rahoto cewa Mai taimaka wa shugaba Muhari wajen harkokin yada labarai na zamani ya saye fam din neman takara.

Abdullahi Muhammad Gaya ya doke hadimin na shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ya samu nasara da aka kubalanci takararsa a gaban kotu.

Da aka je babban zabe a farkon 2023, Mustapha Tijjani Ghali na NNPP ya yi nasara a kan APC. Daga baya Gaya ya samu mukami a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng