EU Ta Janye daga Sanya Ido kan Zaben 2027 a Najeriya? An Ji Yadda Lamarin Yake
- Tarayyar Turai (EU) ta yi martani kan rahoton cewa ta ki amincewa da gayyatar INEC ta sanya ido kan zaben Najeriya na 2027
- Jakadan EU Gautier Mignot ya ce kungiyar za ta tura tawagar kwararrun zabe biyu zuwa hudu Najeriya
- EU ta ce dalilan rashin tsaro da cin zarafin da aka alakanta da janyewarta ba su cikin wasikar da ta aika wa INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da ke Najeriya da ECOWAS ta yi martani kan wasu rahotannin da ke cewa ba za ta sanya ido a zaben 2027.
EU ta karyata rahotannin da ke cewa ta ki amincewa da gayyatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin sanya ido kan babban zaben Najeriya na 2027.

Source: Twitter
Jakadan EU a Najeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, ya nesanta kungiyar daga rahotannin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 10 ga watan Agustan 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa
An ce EU ta ki amsa gayyatar INEC
Rahotannin sun yi ikirarin cewa EU ta ambaci “tabarbarewar rashin tsaro da rashin kyakkyawar mu’amala” bayan tawagar da ta tura domin sanya ido kan zaben 2023 a matsayin dalilan da suka sa ta yanke shawarar kin zuwa.
Wasu kafafen yada labarai da jam’iyyun siyasa, ciki har da Peoples Democratic Party (PDP), sun yada wannan ikirari.
EU ta tura tawagogin sanya ido kan zabuka zuwa Najeriya a dukkan zabukan kasa tun shekarar 2003, lamarin da ya sanya Najeriya cikin kasashen Afirka da kungiyar ta dade tana gudanar da irin wannan aiki a cikinsu.
Gabanin zaben shugaban kasa na Fabrairun 2023, tawagar kwararru 11 ta EU ta isa Abuja a watan Janairu, sannan aka tura masu sa ido na dogon lokaci 40 zuwa sassa daban-daban na kasar.
PDP ta bayyana zargin janyewar EU daga zaben da ke tafe a matsayin “abin tarihi”, tare da cewa hakan na cikin jerin “rashin amincewa da dama daga masu ruwa da tsaki masu muhimmanci kan yadda ake gudanar da zabe a karkashin gwamnatin APC”.
EU ta bayyana matsayinta
Mignot ya ce rahotannin ba daidai ba ne. Jakadan ya ce EU ta tabbatar da cewa ta samu gayyatar INEC a hukumance, ba bukata kawai ba, wadda aka aiko ranar 17 ga Afrilun 2026 domin tura masu sa ido kan babban zaben 2027.
Ya ce a wasikar da EU ta aika wa INEC ranar 28 ga Yulin 2026, kungiyar ta gode wa hukumar kan gayyatar tare da sanar da cewa za ta tura Tawagar Kwararrun Zabe da za ta kunshi kwararru biyu zuwa hudu masu zaman kansu, wadanda za a amince da su a hukumance a matsayin masu sa ido tare da INEC.
A cewar Mignot, tawagar kwararrun zaben za ta tantance ko ana gudanar da tsarin zaben bisa ka’idoji da alkawurran kasa da kasa, na shiyya da na kasa da Najeriya ta amince da su kan gudanar da zabukan dimokuradiyya.
Ya kara da cewa tawagar za ta gabatar da rahoto na karshe mai dauke da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin zabe da zabukan da za su biyo baya. Za a mika rahoton ga gwamnati, kuma idan ta amince, za a iya fitar da shi ga jama’a.

Source: Facebook
EU ta karyata dalilan rahoton
Jakadan ya jaddada cewa dalilan biyu da rahotannin kafafen yada labarai suka ambata ba su cikin wasikar da EU ta aika wa INEC. Ya bayyana wadannan dalilai a matsayin “karairayi kawai”.
Mignot ya ce EU na yanke shawara duk shekara kan irin tawagogin zabe da za ta aika zuwa kasashen abokan huldarta da suka gayyace ta, da kuma irin tawagar da za ta tura, bisa la’akari da halin da ake ciki a kowace kasa da kuma albarkatun da ake da su.
An mika sabuwar bukata ga INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Abdussamad Dasuki, ya mika bukatarsa ga INEC kan zaben 2027.
Abdussamad Dasuki ya bukaci INEC sake duba tsarin gudanar da zaɓen 2027 a ranaku daban-daban, tare da gudanar da zaɓen tarayya da na jihohi a rana guda.
Asali: Legit.ng

