Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini

Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini

- An samu wani lamari mai ban al'ajabi inda matashiya yar shekara 15 ke kukan jini

- Sai dai likitoci sun yi gwaje-gwajensu amma sun kasa gano dalilin da ke sa ta hawayen jini

- Kamar wasa matashiyar ta fara ne da korafin ciwon ciki kafin abun ya zama kukan jini

Rahotani sun kawo cewa likitoci sun gagara gano dalili bayan wata matashiya mai suna Doris, ta shafe fiye da mako guda tana fitar da kukan jini daga idanunta.

An tattaro cewa matashiyar yar kasar Brazil mai shekaru 15 ta kamu da rashin lafiya a ranar 12 ga watan Satumba, sannan mahaifiyarta ta dauke ta zuwa asibiti a birnin Sao Paolo.

Bayan ta yi korafin jin ciwon ciki, sai aka gano tana dauke da tsakuwa a kodarta sannan aka bata maganin rage radadi sannan aka sallame ta zuwa gida.

An dawo da ita zuwa bangaren bayar da kulawa ta gaggawa a ranar Lahadi, bayan jini ya fara zuba daga idanunta. Bata jin ciwo ko radadi sai aka sake mayar da ita gida bayan likitoci sun kasa gano mai ya haddasa zubar hawayen jinin.

Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini
Babbar magana: Likitoci sun kasa gano dalilin da ya sa ƴar shekara 15 ke kukan jini Hoto: Gettyimages
Source: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi

“’Yata ta yi gwaje-gwaje da dama, amma sun kasa gano kowani matsala. Likitocin sun sallame ta sannan muka dawo gida a ranar Litinin,” in ji mahaifiyar yarinyar, Juliana Teixeira de Miranda.

Ta kara da cewa: “Za mu yi duk abunda kwararru suka bukaci muyi, muna son sanin menene matsalar.”

Yan sa’o’i bayan sun koma gida daga asibitin, iyayen yarinyar sun shiga damuwa domin jini na ta kwaranya daga idanunta bibbiyu, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Babu mamaki a gano inda matsalar take idan aka kara komawa asibiti.

Asibitin da aka duba ta sun fitar da jawabi cewa suna bukatar sake wasu gwaje-gwaje domin gano abunda ya haddasa kukan jinin da ba na lafiya ba.

“Likitoci na kiran kasancewar jini a hawaye a matsayin ‘hemolacria’. Maganinshi ya danganta da abunda ya haddasa shi, amma wasu lokutan ya kan daukeda zaran ya bayyana, ba tare da magani ba,” in ji wani likita Rafael Antonio Barbosa Delsin.

“Yawancin lokuta ya kan kasance wata matsala a jikin mara lafiya,” Likita Leandro Fonseca ya bayyana.

KU KARANTA KUMA: Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku

Ya kara da cewa: “koda dai ya kan haifar da wasu abubuwan ban al’ajabi, ba lamari mai wuya bane wajen magani. Ya danganta da abunda ya haddasa shi, ana iya magance shi da maganin kashe kwayoyin cuta. Da wuya wannan matsala ta haifar da wasu matsalolin lafiya ga wanda ya kamu.”

A wani labarin, bidiyon wata karamar yarinya ya bar jama'a da dama baki bude sakamakon hazaka da kaifin basirarta wurin nuna kaunar iyayenta.

A bidiyon mai tsayin minti uku, an ga yarinyar tana bai wa iyayenta shawarwarin zamantakewar aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel