Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya

Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya

- An gano wani likitan kasar Ghana da ba a bayyana sunansa ba yana ta rusar kuka bayan budurwarsa mai suna Ewurama ta yaudari zuciyar shi

- A cikin biyon, an gano marasa lafiya sun yi layi suna jiran shi ya duba su amma matashin likitan ya kasa tausar zuciyarsa a waje daya

- Mabiya shafin soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon wanda tuni yayi fice a yanar gizo

An dauki wani likitan kasar Ghana a wani bidiyo da yayi fice, yana ta rusa kuka kamar karamin yaro bayan budurwarsa ta yaudari zuciyarsa.

Legit.ng ta gano bidiyon mai ban al’ajabi a shafin Instagram din Celebritiesbuzzgh yayinda yake ci gaba da samun tarin sharhi daga mabiya shafin soshiyal midiya.

KU KARANTA KUMA: Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai

Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya
Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya Hoto: celebritiesbuzzgh
Asali: Instagram

A cewar matashin da ya nadi bidiyon, sunan budurwar da ta yaudari matashin likitan Ewurama.

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Likitan na a bakin aiki ne sannan yana da marasa lafiya da yawa da ke jiran ya duba su amma ya kasa tausar zuciyarsa waje guda domin gudanar da aikin da ke gabansa.

Sai dai, abun bakin ciki a bidiyon shine lokacin da ya kai karshe, sai ya fara rera kuka da sauti.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa (hotuna)

A gefe guda, a wani lamari da za a iya kira da sabon salon neman aure, wani matashi dan Najeriya ya nemi auran kyakyawar budurwarsa.

Kasancewar masoyan biyu duk masu yiwa kasa hidima ne wato NYSC, saurayin ya yi suman karya inda yayi kamar ya kamu da ciwon ciki mai tsanani.

Mawuyacin halin da yayi karyan shiga ya sa hankalin budurwar nasa tashi inda ta shiga rudani, tana ta ihun nemawa saurayin nata agaji daga mutanen da ke kallonsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel