Rai dangin goro: Tirela ta markaɗe malamin jami'a tare da matarsa da yaransa 3

Rai dangin goro: Tirela ta markaɗe malamin jami'a tare da matarsa da yaransa 3

- An binne malamin jami'a da tirela ta take tare da matarsa da yayansa su uku a yau Talata, 20 ga watan Oktoba

- Mamatan sun hadu da ajalinsu a ranar 10 ga watan Oktoba bayan motarsu ta yi tawo mu gama da wata tirela a jihar Binuwai

- Jama'a sun sha kuka a lokacin da aka dangana mamatan da gidansu na gaskiya

An binne wani malamin jami’ar Christian University of Mkar, Mkar, Gboko (UMM), Mista Moses Tarnongu, wanda ya mutu a mummunan hatsarin mota tare da matarsa, da kuma yaransu uku a yau Talata, 20 ga watan Oktoba.

An binne su ne a mahaifarsa ta garin Anyamor, kauyen Ikyase, karamar hukumar Gboko da ke jihar Binuwai, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gaba daya ahlin mun mutu ne sakamakon markade su da wata tirela ta yi.

KU KARANTA KUMA: Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato

Rai dangin goro: Tirela ta markaɗe malamin jami'a tare da matarsa da yaransa 3
Rai dangin goro: Tirela ta markaɗe malamin jami'a tare da matarsa da yaransa 3 Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Tirelar dai ta kwace a hannun matukinta inda ta afka kan motarsu kirar Toyota wanda aka faka a wani shingen bincike na yan sanda a hanyar babban titin Ugbema- Ushongo a ranar 10 ga watan Oktoba, a jihar Binuwai.

Daruruwan masu alhini sun hallara a wajen binne gawar mamatan.

Jama’a da dama a wajen na ta kururuwa da kuka yayinda aka sada mamatan da gidansu na gaskiya.

KU KARATA KUMA: Buhari na da ‘ya’ya, ya san yadda halin matasa yake – Obasanjo ya yi magana kan #Endsars a karon farko

A wani labari na daban mun kawo maku cewa, Allah ya yi wa jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa, Alhaji Adamu Muhammad rasuwa.

Muhammadu ya rasu a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Yola, inda ya kwashi dan lokaci yana jinya.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya mika ta’aziyyarsa ga jam’iyyar APC a kan rasuwar jigon nata, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng