Hoton kafin aure ya jawa saurayi da budurwa caccaka a wajen yan Najeriya
- Wasu masoya sun zabi amfani da sabon salo wajen daukar hoton kafin aurensu, inda suka dauke shi a kan hanyar jirgin kasa
- A hoton, mijin ya yi kamar yana baiwa amaryar tasa iskar shaka ta Oksijin
- Masu amfani da shafin Twitter sun gaza boye rashin jin dadinsu a kan wannan hoto da ya shahara
Wasu masoya yan Najeriya sun sha gagarumin suka bayan bayyanar hoton kafin aurensu wanda ya shahara a shafin Twitter.
A hoton wanda ya haddasa cece-kuce a yanar gizo, an gano ma’auratan tsaye a kan hanyar jirgin kasa, yayinda matashin ya daura zani a kugunsa, ita kuma amaryar ta nada nata a wuya kamar riga.
Matashin, wanda ya tsaya dan tazara kadan tsakaninsa amaryar tasa, yana sanye da na’urar aika iska ta oksijin zuwa ga matashiyar.
Manufar da ke tattare da hoton shine cewa matashin zai kasance tare da amaryar tasa duk rintsi duk wuya.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Gwamnonin arewa maso gabas sun goyi bayan amfani da sojin haya
Sai dai, sam abun bai burge masu amfani da shafin Twitter ba inda suka yi ta yamutsa gashin baki a shashin yin sharhi.
Wani mai amfani da shafin Twitter @the_writa ya rubuta:
“Shin wannan yana nufin amfani da Oksijin guda ne ko me? Akwai wani karin bayani? Wannan shawarar wanene? Ina iyayensu ko manya a ahlinsu? Kamar yadda mahaifiyata ta kan yi ihun fadi a karnin baya idan mu yaranta muka yi kuskure ‘ina bulalan?!”
@tesswhyteT ta ce:
“Kan daraktan shirin ya kulle ruf. Babban bata.”
@Juliet81849901 ta rubuta:
“Allah ya kyauta... Wai wa ke ba wadannan ma’auratan wadannan shawarwari na yin irin wannan hoton kafin auren dan Allah?"
KU KARANTA KUMA: Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashin tsaro
A wani labarin, wata yar kasuwa, Nafisat Olajire, a ranar Litinin, ta shigar da kara wata kotun gargajiya da ke Ibadan domin a raba aurenta na shekaru 18 da mijinta, Sarafa Olajire, saboda yana yawan yunkurin murde mata wuya.
Ta ce sai da likitoci suka shiga lamarin kafin ta farfado, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng