Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu

Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu

- Bidiyon wani mutumi yayinda yake kokarin raba fada tsakanin kaji biyu ya yi fice a shafin soshiyal midiya

- Mutumin ya yi wa kajin fada yayinda ya rike su, sannan ya ture kowannensu gefe

- Jim kadan bayan mutumin ya dan matsa sai kajin suka sake far ma junansu da hari yayinda shi kuma ya ci gaba da ture su

Wani mai amfani da shafin soshiyal midiya, Tumi Sole ya wallafa bidiyon wani mutumi yana raba fada a tsakanin kaji biyu.

Bidiyon mai tsawon sakwan 30 ya fara ne da nuno mutumin rike da kaji a dukka bangarorinsa biyu na hagu da dama yayinda yake yiwa daya daga cikinsu magana.

Sai kuma ya juya kansa don yi wa daya kazan shima fada. Chan kuma sai ya shiga tsakaninsu inda ya sake su. A nan ne kuma sai fada ya sake barkewa a tsakanin kajin. Ga dukkan alamu dai ba za su iya barin junansu ba.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023

Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu
Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu Hoto: @tumisole
Asali: Twitter

Sai suka fara caccakar junansu yayinda mutumin ya ci gaba da kasancewa a tsakaninsu. Abun ya bashi haushi yayinda ya fara yi masu ihu.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi kan bidiyon:

@CeliShongwe ta wallafa: "Abun da ban dariya sosai, za ka rantse da mutum yake magana.”

@juju_moate ya wallafa: "Kuma suna da fitina.”

@itsKamoBruv ya rubuta: "Shakka babu wadannan @ChickenLickenSA vs @NandosSA ne suke fada a unguwannin Twitter.”

KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

A wani labari na daban, an sayar wa wani dan kasar China da wata tsuntsuwa wacce suke kira New Kim a ranar Lahadi.

A kasar Belgium, ana sayar da tsuntsuwar tsere, wacce suke kira da New Kim a kalla euros miliyan 1.6, wanda yayi daidai da N729,479,670.40.

Wani babban dan kasuwa mai harkokin tsuntsaye ya siyar da tsuntsun a wani taro da aka yi ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, kamar yadda Indian Express suka ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng