Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)

Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)

- Wata yar Najeriya mai sun a Fehintoluwa Okegbenle ta nuna cewa mutane na iya cimma duk wani abu da suka sa a gaba idan har sun yarda da kansu

- Okegbenle ta yi wani tafiya zuwa Abuja kan babur kuma cikin nasara sannan ta kai inda za ta cikin sa’o’i 13

- Matashiyar ta ce an yi ta sanyaya mata gwiwa a lokacin da ta shirya yin tafiyar, amma sai ta ki janyewa

Wata yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin murnar nasarar da ta samu bayan ta yi tattaki daga Lagas zuwa Abuja a kan babur.

Matashiyar mai suna Fehintoluwa Okegbenle ta wallafa wasu hotunanta da na sauran mutane da suka yi tafiyar a shafinta na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Kungiya ta rubutawa Shugabannin Intel takarda bayan an kori Ma’aikata 600

Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)
Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 Hoto: @FehinLean
Asali: Twitter

A cewarta, ya dauke su tsawon sa’o’i 13 kafin suka kai Abuja a kan babur. Ta ce mutane sun sha sanyaya mata gwiwa a lokacin da ta shirya yin tafiyar, amma sai ta ki bayar da kai bori ya hau.

KU KARANTA KUMA: Kada ku sa mu yadda cewa wadanda aka lallasa a zaben 2019 ne suka bullo da EndSARS - Hadimin Buhari ga dan Atiku

Da ta wallafa hotunan, Okegbenle a shafinta na @FehinLean ta rubuta:

“Tafiya daga Abuja zuwa Lagas a kan bun hawa mai kafa biyu. Ya dauki tsawon sa’o’i 13. Na gwada fasahata, juriyata, da karfina gaba daya. Kun gani, idan baka yarda da kanka ba babu wanda zai yarda da kai.

“Na samu masu sanyaya mani gwiwa da dama a kan wannan tafiyar amma ban bayar da kai bori ya hau ba ta kowani gefe. Ina ne gaba?”

A wani labari na daban, zanga-zangar neman a kawo karshen rundunar SARS ya dauki sabon salo a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, lokacin da wani matashi mai suna Demola ya nemi auran budurwarsa a wajen taron.

Idan za ku tuna dai ana gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kan neman a soke rundunar SARS sakamakon zarginsu da ake yi da cin zarafin al’umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel