Tsohon Ministan Buhari Ya Maka ADC Kotu bayan Rasa Tikitin Gwamna
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 29 ga Satumba domin sauraron karar da Mohammed Hassan Abdullahi ya shigar kan zaben fidda gwani na ADC a Nasarawa
- Kungiyar yakin neman zaben tsohon ministan ta ce ta yi watsi da ayyana Nuhu Angbazo a matsayin wanda ya lashe zaben
- John Mathew ya ce za su ci gaba da shari’ar har zuwa kotun karshe idan hakan ya zama dole domin samun adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - An sanya ranar 29 ga watan Satumba domin sauraron karar da tsohon ministan muhalli, Mohammed Hassan Abdullahi, ya shigar kan sakamakon zaben fidda gwamnan African Democratic Congress (ADC) a jihar Nasarawa.
Za a saurari karar da tsohon Ministan ya shigar a babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a dakin shari’a na biyar.

Source: Twitter
Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben MHA, Barrister John Mathew, ne ya bayyana hakan a Keffi bayan wani taro da kungiyar yakin neman zaben tsohon ministan ta gudanar, cewar rahoton Daily Trust.
Mathew ya ce an riga an kai wa dukkan bangarorin takardun shari’ar, kuma sun yi musayar takardu, sai dai an samu tsaiko sakamakon hutun shekara-shekara na kotuna.
An yi watsi da sakamakon zaben
Kungiyar yakin neman zaben ta sake jaddada cewa ta “yi watsi kwata-kwata da ayyana Manjo Janar Nuhu Angbazo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na ADC”, tana mai cewa “bai ci zaben ba”.
Ya bayyana shari’ar a matsayin “ta musamman”, yana zargin cewa jam’iyyar ta soke sakamakon wata karamar hukuma baki daya inda Abdullahi ya samu fiye da kuri’u 10,000.
A cewarsa, an soke sakamakon ne bisa zargin cewa an samu tashin hankali, duk da cewa akwai wani rahoton hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da aka tabbatar wanda yake gaban kotu.
Ya ce rahoton ya bayyana cewa an sanya ido kan zaben a dukkan mazabu 11, kuma an gudanar da zaben cikin lumana.
An gabatar da sakamakon gaban kotu
Mathew ya ce sakamakon da aka soke yana daga cikin shaidun da aka riga aka gabatar gaban kotu.
Ya ce kungiyar za ta dage wajen ganin an yi adalci, tare da alkawarin ci gaba da shari’ar har zuwa kotun karshe a Najeriya idan hakan ya zama dole.
“Za mu dage cewa a yi adalci, kuma za mu kai wannan shari’a har zuwa kotun karshe a Najeriya, idan hakan ya zama dole. Don haka, ba mu amince da shi a matsayin dan takarar ADC ba saboda bai ci wani zabe ba,” in ji shi.
Ba za a yi sulhu ba tukuna
Da aka tambaye shi kan yiwuwar sulhu tsakanin bangarorin, Daraktan Janar din ya ce ba za a iya fara tattaunawar sulhu ba matukar ana ci gaba da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ya yi misali da cewa mutum ba zai karbi abin da wani ya mallaka ba, yana rike da shi a hannu daya, sannan ya mika dayan hannun yana neman afuwa da sulhu ba.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa

Source: Original
Mohammed Hassan Abdullahi ya taba rike mukamin ministan muhalli a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kuma tsaya takarar zaben fidda gwamnan ADC a jihar Nasarawa, inda jam’iyyar ta ayyana Nuhu Angbazo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ana zargin sauya dan takarar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa rigima na neman kunno kai a jam'iyyar ADC a jihar Adamawa kan batun sauya dan takarar gwamna.
Rade-radi suna yawa cewa ADC ta maye gurbin Suleman Umar wato Omarana da Modibbo Hamman Tukur Ribadu a shafin INEC.
Asali: Legit.ng

