Za a daure bawan Allah da ya bindige zakara
- Wani mutumi dan kasar Faransa zai sha daurin shekaru biyar a gidan maza
- Kotun kasar ta yanke masa wannan hukunci kan harbe wani zakara da yayi saboda kawai ya dame shi da cara
- Mai zakaran ne ya shigar da karar inda ya nemi a bi ma dabban nasa hakkinsa
Rahotanni sun kawo cewa an zartar da hukuncin daurin shekaru biyar a kan wani mutumin kasar Faransa sakamakon kama shi da laifin bindige wani zakara tare da tsire shi da karfe saboda ya dame shi da cara.
Makwabcin zakaran wanda aka ambata da suna Marcel wanda ya fito daga jihar Ardèche, ne ya harbe shi a watan Mayu bayan carar da yake yi ya fusata shi.
Mammalakin zakaran, Sebastien Verney, shine ya rubuta wata takarda don neman a bi wa zakaransa hakki.
Kuma tuni akalla mutane dubu dari daya suka rattaba hannu a kan takardar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba
An kuma kama makwabcin nasa da aikata laifin yi wa dabba mugunta da sauran laifuka.
Baya ga hukuncin dauri da aka yanke masa, an kuma ci tararshi kudi €300 tare da dakatar da shi daga rike duk wani maƙami tsawon shekara uku.
A cewar mai zakaran, Mista Verney: "Wannan ba zai taɓa gyara abin da ya aikata ba.”
A takardar karar da ya rubuta, ya yi magana kan "mummunan abin bakin ciki" da ya fada wa iyalan, yayin da ya yi kira a kan cewa kada kauyuka su zama wurin ajiyar kayan tarihi.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari
"Su waye za su sake fadawa cikin wannan barazana? Tattabarun da ke kuka, girbin alkama, noman tumatir, kukan jaki, kararkƙararrawar agogo ko kuma kiwon shanu?"
Wannan ita ce takaddamar da ta shafi zakara da ta mamaye kafafen yada labarai a baya-bayan nan a kasar Faransa.
A wani labari, kungiyar sa Ido kan hakkin dan adam (SERAP) na shirin shigar da kara a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Najeriya kan bukatar karbo bashi daga kudaden fansho.
Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta yi wannan sanarwar ne a cikin wani wallafa da tayi a shafin Twitter a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.
SERAP ta kuma bukaci yan Najeriya da su nuna ra’ayinsu ta hanyar bayyana cikakken sunayensu domin shiga sahun masu kara wanda za a shigar nan da kwanaki 14.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng