Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ‘yan uku da ta haifa saboda kudin asibiti

Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ‘yan uku da ta haifa saboda kudin asibiti

- Wani magidanci ya tsere ya bar matarsa da 'yan uku da ta haifa masa saboda kudin asibiti

- An tattaro cewa ma'auratan wadanda talauci ya yi masu katutu suna da yara hudu kafin Allah ya sake azurta su da yan uku

- Mijin ya kuma sha alwashin cewa ba zai dawo ba har sai an sauke masa nauyin kudin asibitin

Wani magidanci mai matsakaicin shekaru ya yasar da matarsa da ke jego, Evelyn, a wani asibitin kudi da ke Okpoko, karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra, inda ta haifi yan uku.

Sunday Odinake, dan asalin Ubaraekwem da ke yankin Ihiala, ya gudu ya bar gidansa na No. 153b Obodoukwu Road saboda bai da karfin biyan kudin asibiti.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa tuni ma’auratan suka haifi yara hudu wadanda aka cire daga makaranta saboda rashin kudin biyan makarantar.

Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ‘yan uku da ta haifa saboda kudin asibiti
Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ‘yan uku da ta haifa saboda kudin asibiti Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Ya ce: “Kafin na haifi yan uku, babu abinci a gidan. Ina siyar da ruwan leda sannan mijina bai da aiki, wasu lokutan ya kan yi yan buga-buga wanda daa ciki ne muke cin abinci.

KU KARANTA KUMA: Soyayya ruwan zuma: Labarin yadda wani mutum da aka haifa da tawaya ya hadu da kyakyawar matarsa

“Muna rayuwar neman na sawa a bakin salati ne sai kuma ga zuwan yan uku sannan lamarin ya kara tabarbarewa. Mijina na ta korafin yadda zai iya daukar nauyinmu tunma kafin na haihu, inda yake zaton da daya zan haifa.

“Amma ganinsu su uku, gashi muna da yara hudu dama, sai ya gudu. Kimanin makonni biyu kenan. Abun bakin ciki, bashi da waya balle a neme shi ta nan.

“Ina da tabbacin mijina ya yasar da mu ne saboda kudin asibiti N450,000 da aka nemi ya biya domin a mayar da ni asibitin kwararu sakamakon matsala da na samu.”

Misis Odiunaka ta ce yarta wacce ke zuwa gida tana kawo masu ruwan zafi na wankan yan ukun ta ce bata ga mahaifinta ba.

Ta kara da cewa: “yarinyata ta ce wani ya fada mata cewa mahaifinta ya rantsare ba zai dawo ba har sai ya tabbatar da an biya kudin asibitin.”

Koda dai mai jegon ta yi nasarar hada N50,000 daga yan uwa da abokan arziki, ta roki matar gwamnan jihar, Misis Ebelechukwu Obiano, da ta taimaka mata.

KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

“Kafin mijina ya tsere, ya gabatar da wata wasika zuwa ga matar gwamna da ofishin kwamishinar harkokin mata da jin dadin kananan yara, cewa na haifi yan uku kuma ina bukatar taimako, amma babu amsa. Kila wannan ne ya sa shi guduwa saboda matsi,” in ji ta.

A gefe guda, bidiyon wata kyakyawar amarya ya sanya yan Najeriya da dama dariya a shafin soshiyal midiya.

A bidiyon wanda Legit.ng ta samo a shafin Instagram, an gano amaryar da angonta suna ta dauke dauken hotunan auransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel